Tsohon Sanatan Bauchi Ta Kudu, Sanata Lawal Yahaya Gumau ya rasu a daren ranar Asabar bayan fuskantar wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekaru 57 a duniya. Ya bar mata biyu da yara 8. Ya kuma rasu ne a Abuja.
Tsohon hadiminsa, Kwamared Haruna Usman Muhammad, shi ne ya tabbatar da rasuwar nasa ga wakilinmu a safiyar Asabar ɗin nan.
- Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
- Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (8)
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, Sanata Lawal Gumau ya fara zama a kwaryar majalisar dattawa ne a 2018 bayan da ya samu nasara a zaɓen cike gurbin kujerar sanatan biyo bayan rasuwar Sanata Ali Wakili da ke kan kujerar a wancan lokacin. Ya sake samun nasara aka zaɓe shi a babban zaben 2019 har zuwa 2023.
Sai dai duk ƙoƙarin da Lawal Yahaya Gumau ya yi na zarcewa a matsayin sanata a 2023 lamarin ya gagareshi har ta kai ya fice a APC ya shiga NNPP domin yin takara amma bai samu nasara ba. Daga baya ya koma jam’iyyar PDP bayan kammala zaɓen 2023.
Kafin ya zama sanata, ya yi majalisar dokokin ta tarayya da ya wakilci mabazar Toro daga 2011 zuwa 2018.
An shirya masa jana’iza da ƙarfe 1pm a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairum 2025 a Masallacin da ke kofar gidansa da ke Gwarimpa, Abuja.
Cikakken labarin daga baya:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp