Da safiyar Litinin din nan ne Hukuma Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar da Kwankwaso ke mara wa baya, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a jihar a ranar Asabar da ta gabata.
Abba ya samu ƙuri’u 1, 019, 602 inda ya doke babban abokin karawarsa, mataimakin Gwamna Ganduje, Dakta Nasiru Gawuna wanda ya samu ƙuri’u 890, 905. Sai kuma ɗan takarar PDP da ya zo na uku da ƙuri’u 15, 957.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp