Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata batun cewa ya karya darajar Naira inda Dala 1 ta koma Naira 630.
CBN ya ce labarin da Jaridar Daily Trust ta bayar ba gaskiya ba ne, tunani ne kawai irin nasu.
Bankin ya ce ko a yau da safe ana sayar da Dala 1 a kan Naira 465 a kasuwar canjin kuɗi na gwamnati.
Don haka bankin ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya su yi biris da labarin saboda ba shi da tushe balle makama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp