Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, Daliban makaranta da ‘yan bindiga suka kwashe a garin Kuriga sun shaki iskar ‘yan ci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a kafar sada zumuntarshi ta X (twitter) a farkon sa’o’in ranar Lahadi.
- Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Ɗaliban Kuriga Na Neman Fansar Naira Tiriliyan 1
- Shugaban Kasar Nauru Zai Ziyarci Kasar Sin
“Ina so in sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga,” in ji Gwamna Uba Sani.
“Muna godiya ta musamman ga mai girma shugabanmu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR kan yadda ya ba da fifiko kan tsaro da tsaron ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da ganin an sako yaran makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani rauni ko lahani ba.
“Yayin da yaran makarantar ke tsare, ya damu matuka da irin damuwarmu, ya yi aiki ba dare ba rana tare da mu don ganin an dawo da yaran lafiya.”
In ba a manta ba, an yi garkuwa da yaran makarantar ne a ranar 7 ga watan Maris lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye makarantun firamare da Sakandaren da ke garin.
Wani malami a makarantar, Sani Abdullahi, ya ce, dalibai kusan 287 ne aka nema aka rasa bayan harin.