Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya gana a jiya Litinin da babban mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasar Japan, Takeo Akiba a nan birnin Beijing, inda suka amince da ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a matakai daban daban.
Hakika bayan tankiya da takalar da aka gani daga bangaren Japan a baya-bayan nan, musamman game da batun zubar da dagwalon nukiliya cikin teku, irin wannan tattaunawa ta jiya, tana nuna alamun cewa, Japan na son gyara kuskuren da ta tafka a baya.
- An Bude Baje Kolin CIIE Karo Na 7 A Birnin Shanghai
- Kasar Sin Ta Daukaka Kara Zuwa WTO Game Da Hukuncin Karshe Kan Matakin EU Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin
Tarihi bai taba nuna inda rikici ya haifar da zaman lafiya ba. Da alama sabon firaministan Japan Shigeru Ishiba, ya fahimci hakan, sannan ya san hakkin makwabtaka, kuma yana kuma son gyara kuskuren kasarsa da ma dangantakar da ta yi tsami tsakaninta da Sin.
Zuwa yanzu, na san kowa ya fahimci cewa, kasar Sin tana mayar da hankali ne kan kare kanta da muradunta da kuma neman sulhu cikin lumana maimakon tsokana da tankiya da fito-na-fito. Haka kuma, kullum a shirye take wajen ganin an hada hannu an wanzar da zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya. Kuma ba shakka idan Japan ta nemi zaman lafiya da Sin, to tabbas Sin tana maraba da hakan.
A baya, Japan ta yi biris da kuken al’ummarta da na makotanta, inda ta bari wasu kasashe daga wajen su na amfani da ita domin cimma wasu muradu na kashin kai da kokarin ta da rikici tsakanin Sin da kasashe makwabtanta. Amma idan har a yanzu Japan ta fahimci hakan ba hanya ce mai bullewa ba, to za a samu zaman lafiya da ci gaban da ake muradi, sannan wasu daga waje ba za su samu damar tsoma baki da haifar da rikici a yankin ba.
A wannan gaba da ake tattaunawa, ya kamata Japan ta girmama makwabtanta, ta kuma dauki korafinsu da muhimmanci domin samun fahimtar juna da kuma kyautata alakarta da su. Kamar yadda Wang Yi ya bayyana, dangantakar bangarorin biyu na wata gaba mai muhimmanci, don haka, ya kamata Japan ta mutunta kudurinta kan batun Taiwan da kuma daukar Sin a matsayin makwabciya kuma abokiyar hulda maimakon barazana ko abokiyar adawa. Kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorin biyu, za ta taka muhimmiyar rawa ga ci gabansu da zamantakewar al’ummarsu da ma yankinsu baki daya. (Fa’iza Mustapha)