Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS) ta kama shugaban karamar hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa Hon. Joshua Zheyekpuwudu da tarin takadun zabe na bogi wadanda aka dangwale.
Lamarin ya faru ne a yau Asabar a zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki da ke gudana.
- Ina Da Kwarin Guiwar Lashe Zaben Gwamnan Bauchi -Sanata Jika
- Da Dumi-Dumi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti, Egbeyemi, Ya Rasu
Jami’an tsaron sun kama Shugaban karamar Hukumar ne a unguwar Tudun Kwauri dake Lafia a jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa inda za shi.
A halin yanzu dai Hon. Zheyekpuwudu yana hannu jami’an tsaro.
Sai dai a Jihar Nasarawa ana gudanar da zabe lami lafiaya zuwa yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp