Hukumar INEC ta shelanta dan takarar Gwamnan Jihar Kebbi na Jam’iyyar APC, Idris Nasiru a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar.
Jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan shi ne ya shelanta hakan da ranar yau Lahadi bayan kammala sake zaben gwamnan da aka kammala a ranar Asabar a wasu rumfunan zabe da ke jihar.
Nasiru dai kamar yadda INEC ta shelanta ya samu nasara ne da kuri’u 409,225 da hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP, Bande Aminu da ya samu kuri’u 360,940
Cikakken labarin na tafe
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp