Dalibai mata takwas da aka yi garkuwa da su a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Awon a karamar hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun tsere daga sansanin ‘yan ta’addan.
‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da daliban ne a ranar Litinin, 3 ga Afrilu, 2023 a Awon, karamar hukumar Kachia.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce bisa ga bayanan sirri da aka samu, daliban sun tsere ne daga wani dajin da ke kusa da kan iyakokin Kaduna da Neja.
Aruwan ya ce daliban sun yi tafiya na kwanaki kafin su isa wani wuri da ke da aminci wanda ba a bayyana sunan wurin ba sabida dalilan tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa daga bisani majiyoyin leken asiri sun sanar da gwamnatin jihar cewa, a yi gaggawar kwashe daliban daga garinsu.
Aruwan ya ci gaba da cewa Gwamna Nasir El-Rufai bayan samun bayanan sirrin, ya umurci ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida da ta tuntubi runduna ta 1 ta sojojin Nijeriya domin kwashe daliban cikin gaggawa zuwa babban birnin Kaduna, sabida an tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kuduri aniyar sake sato daliban ta kowane irin hali.
Ya kara da cewa “An kwashe daliban zuwa wani wurin sojoji inda a yanzu haka suke samun kulawar likitoci.”
A halin da ake ciki, Gwamna El-Rufai ya bayyana jin dadinsa da samun wannan rahoto, kuma ya yabawa daliban bisa nuna jajircewa wajen ganin sun kubuta daga hannun ‘yan ta’addan.