Wasu dalibai yanzu haka suna kan gudanar da zanga-zanga a Gusau babban birnin jihar Zamfara bisa garkuwan da wasu ‘yan bindiga suka yi ma wasu dalibai guda biyar.
Masu zanga-zangar wadanda mafi yawansu daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau ne, sun rufe kan babban hanyar Zariya zuwa Sokoto domin nuna damuwarsu da halin da suke ciki a yau Asabar.
- Rashin Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Nemi Taimakon Babban Hafsan Tsaron Kasa
- Gwamnan Zamfara Ya Bukaci Hadin Kan Sabbin ‘Yan Majalisar Jihar
Wannan lamarin ya janyo matuka motoci da fasinjoji tsayuwar dole domin babu hanyar wucewa
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka Jima suna fama da matsalar masu garkuwan da mutant domin neman kudin fansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp