Tsohon Sanata, Dino Melaye, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kogi.
Melaye ya samu kuri’u 313 inda ya doke abokin takararsa, Idoko Ilonah wanda ya samu kuri’u 124.
Melaye zai fafata da Ahmed Ododo dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp