Gidajen mai na kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) sun kara farashin man fetur.
Man da a baya ake sayar da shi kan Naira 897 a Abuja, babban birnin kasar, a halin yanzu ana sayar da shi kan Naira 1,030 kan kowacce lita.
- Boko Haram Sun Sake Kai Wani Hari Kan Al’ummar Kirawa A Jihar Borno
- Kare Hakki Da Rayukan Mutane Ba Batu Ne Na Siyasantarwa Ko Nuna Fuska Biyu Ba
A Legas, man da a da ake sayar da shi kan Naira 885 kan kowace lita, yanzu ana sayar da shi kan Naira 998 kan kowacce lita.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da muka bayar da rahoton cewa, akwai yiwuwar hauhawar farashin man fetur sakamakon ficewar kamfanin na NNPC daga dillancin man fetur daga matatar man Dangote.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp