Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS).
Mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2018.
Cikakkun bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp