Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamola, ya mika jerin sunayen ministocin shugaba Bola Tinubu ga majalisar dattawa a zaman da ta yi yau, ranar Alhamis.
An shigar da Gbajabiamila a cikin majalisar ne da misalin karfe 1:18 na rana don isar da sakon jerin sunayen ga majalisar.
Gbajabiamila ya mika jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa, God’s Akpabio, sannan ya yi musabaha da wasu Sanatoci kuma ya bar zauren majalisar da misalin karfe 1:30 na rana.
Akpabio ya karanta sunaye 28 ba tare da bayyana jihohinsu ko ma’aikatarsu ba kamar yadda mutane da yawa suka yi tsammani.
Akpabio ya ce kwamitin majalisar zai tantance kashin farko na sunaye 28 a lokaci guda kafin kashi na biyu ya iso kamar yadda shugaba Tinubu ya bayyana a takardar kashin farko.
Ga sunayen kamar haka:
- Abubakar Momoh
- Amb. Yusuf Tuggar
- Arc. Ahmed Dangiwa
- Barr. Hannatu Musawa
- Chief Uche Nnaji
- Dr. Binta Ilu
- Dr. Doris Uzoka
- Senator David Umahi
- Nyesom Wike
- Mohammed Badaru Abubakar
- Malam Nasir El-Rurai
- Hon. Nkiru Onyecheacha
- Hon. Olubunmi Tunji Ojo
- Hon. Stella Okotete
- Hon. Uju Kennedy
- Bello Mohammed Goronyo
- Dele Alake
- Lateef Fagbemi, SAN
- Muhammad Idris
- Waheed Adebayo Adelakun
- Olawale Edun
- Iman Suleiman Ibrahim
- Prof. Ali Pate
- Prof. Joseph Useh
- Senator Abubakar Kyari
- Senator John Enoh
- Senator Sani Abubakar Danladi
- Hon. Ekperipe Ekpo