Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aminsa da canza wa Injiniya Abubakar Momoh daga kasancewar ministan ma’aikatar matasa zuwa ma’aikatar bunkasa shiyyar Niger Delta.
A sanarwar da kakakin shugaban kasan, Ajuri Ngelale ya fitar a daren ranar Lahadi, ya ce za a sanar da sabon ministan da zai jagoranci ma’aikatar matasa nan kusa kadan.
Ya ce, ministocin da tura ma’aikatar sufuri, harkokin cikin gida da na Marine & Blue an canza musu ma’aikatu.
Sanarwar ta ce, “An canza wa Adegboyega Oyetola ma’aikata zuwa ma’aikatar Marine & Blue Economy.
“Hon. Bunmi Tunji-Ojo shi kuma aka sake turawa a matsayin ministan kula da harkokin cikin gida.
“Hon. Sa’idu Alkali shi kuma an sauya masa ma’aikata zuwa matsayin ministan ma’aikatar sufuri na tarayya.”
“Bugu da kari, dukkanin ministocin da ke bangaren mai da iskar gas yanzu za su kasance a ma’aikatar albarkatun mai ta kasa kamar haka:
“Sanata Heineken Lokpobiri shi ne karamin ministan kula da albarkatun Mai.
“Hon. Ekperipe Ekpo shi kuma karamin ministan kula da albarkatun iskar gas.”
Ya ce dukkanin sauye-sauyen sun fara aiki ne nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp