Kazalika mun samu zantawa da daya daga cikin ‘yammatan gidan, da ta yi magana da yawun shugabar ‘yammatan gidan, bayan da muka nemi jin ta bakin shugabar matan amma ba mu same ta ba, ta bayyana mana sunanta da abin da ya fito da ita daga gida, inda ta ce ta ji sha’awar wannan sana’a ce ta hanyar wata kawarta da suka hadu a shafin sada zumunta na Faccebook.
A ta bakinta…
Sunana Karima Bala daga Gwagwalada, kawai gani na yi wannan sana’a ta ban sha’awa, amma ba don na rasa ci da sha da sutura a gidammu bane. Kawai dai ina sha’ar abin ne idan na zo kallo, don haka sai abin ya ban sha’awa kawai ina son wasan a rayuwata.
Ba saboda auren dole ta bar gidansu ba…
Ni dai ba a taba cewa za a yi min aure ba ballantana na gudu, kuma harkar makaranta babana yana kokari, kawai dai na yi sha’a ce saboda na hadu da aboki a shafin sadarwar zamani, to muna hira da ita sai ta nuna min yanayin harkar da take yi.
Da farko dai ban gaya wa iyayena inda zan ce na ce musu dai zan je makaranta sai na taho wurinta.
Da na zo na yi wasa na kamar sati daya ban koma gida ba, an nemi ba a ganni ba, daga baya aka gano inda nake aka zo aka mayar da ni gida.
Yanzu dai ina da kyakkyawar fahimtar juna ni da iyayena, idan zan zo nan sai in ce mata Momcy ina son zuwa gidan Dirama kuma na taho.
Irin zaman da suke yi a gidan dirama…
Ni in na ce zamana a gidan Basulo ban ji dadi ba gaskiya na yi karya, saboda da ban ji dadi ba idan na tafi ba zan kara dawowa ba, ya danganta da yadda kika dauki kanki, idan ba ki da godiyar Allah dole ne ki zama daban.
Gaskiya ne wata tana sa wa rayuwarta cewa ita kawai ta fito ne bariki ta yi shaye-shaye, ko namiji ya kwana da ita ba ta damu da wani kasuwanci ba, amma a wadanda suka dauki harkar da muhimmanci namiji idan yana son ki, to kawai ya nuna miki gata yayin da kika hau dakalin da kike nuna bajinta.
Abin da ta samu a gidan dirama…
A gaskiya a fitowata harkar wannan wasa, an yi biki, da kudin na biya wa kanwata kudin jarabawar NECO da WAEC, inda kawata a Nasarawa ta yi cikon Naira 150,000 ta zana wannan jarrabawar.
Burinta…
A halin yanzu ba ni da burin da ya wuce na taimaka wa kannenna su ci gaba da karatu don haka ne na ajiye nawa karatun domin samun kudin da zan tallafa wa kannena su su yi gaba, domin iyayenna ba su karfin daukar nauyinsu. Kuma ina kira ga abokan aikina da su zauna lafiya da abokan arzikinsu.