Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, a yau zan yi waiwaiye kan abin da ya shafi mulkin jihar kano.
- ‘Yansanda Sun Gayyaci Shamakin Kano Kan Zargin Karya Dokar Haramta Hawan Sallah
- Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin HaÉ“aka Jama’ar Kano
Mun fi ƙaunar zaman lafiyar mutanen kano, kanon ta zauna lafiya, akan wata kujerar mulki ta mukamin gwamnati ko sarauta ta kowane ne, duk wanda ke rike da wani mukami darajar kanon na zaune lafiya ya samu.
Idan wani abu na masifa ya tunkaro mu Allah ya kawo mafita da kariya, addu’a ya kamata mu yi ba shiririta ba da surutan da basu da amfani ba, da yawa daga cikin masu mukaman sun fi kaunar kujerunsu akan zaman lafiyar jihar, ba fata ake yi ba idan wata masifar ta afku dukkanninsu kwashe iyalansu za su yi su bar kasar, domin suna da inda za su kai iyalansu, ku ko ina za ku kai naku iyalan?
Ya kamata mu yi hankali wallahi wallahi kano ba a daidai muke ba, muna takama da malamai amma wani sanadi na siyasa ya sa mun zubar da darajarsu, kowanne jahili babba ko yaro zai fada musu magana ta yadda ya ga dama,
Malamai magada Annabawa ne, dole ka yarda ko ka zama jahili, da yawa daga cikin masu rike da mukaman da suke hana mu zaman lafiya shekarunsu sun tafi sun girma, ko ammanta sittina ko saba’una ake yi yanzu, daga karshe muna rokon ku da kanku ku nemawa jihar abun da za ta yi alfahari da ku bayan babu ku, domin Dole za ku mutu ku bar jihar da mutane a ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp