• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Na Gaba Ake Gane Zurfin Ruwa

by CGTN Hausa
2 years ago
Ruwa

A watan Satumba na shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin na da burin kawar da sinadarin carbon dioxide kafin shekarar 2030, da kuma cimma matsaya game da kawar da iskar carbon gaba daya kafin shekarar 2060. A watan Nuwamban bana, a taron San Francisco, Sin da Amurka sun yanke shawarar yin hadin gwiwa a karkashin kungiyar aiki kan inganta yanayi. La’akari da ayyuka masu inganci wadanda ba a taba yin irinsu ba game da inganta yanayi, Sin ta zama babbar mai shiga tsakani, mai ba da gudummawa, kuma jagora a harkokin yanayi na duniya. Shi ya sa kasashen duniya suka sallama ma kasar Sin jagorancin magance sauyin yanayi saboda da na gaba ake gane zurfin ruwa.

Tarihi ya tabbatar da irin gwagwarmayar da kasar Sin ta yi kafin ta kai ga wannan matsayi na jagora a harkokin inganta yanayin duniya. A zamanin da, gidajen wanka na jama’a inda za ka biya kudi kadan sa’annan ka yi wanka da ruwan zafi sun kasance “ababen kallo” na musamman a biranen kasar Sin. Saboda ba a cikin sauki ake iya samun ruwan zafi na wanka a gidajen mutane ba.

  • An Rufe Taron Fahimtar Sin Na shekarar 2023
  • Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu Sun Sake Karfafa Huldar Diflomasiyya

Amma a yau, wadannan gidajen wanka na jama’a wadanda ke fitar da iskar carbon mai dumama yanayi suna zama tarihi a hankali. Ci gaba a fannin fasahar samar da na’urar dafa ruwa mai amfani da hasken rana ta kawo sauki ga al’umma wajen samun biyan bukata ba tare da gurbata muhalli ba wanda ya daidaita kasar Sin a kan turbar rayuwa mai karancin iskar carbon.

Daga kayan masarufi masu aiki da makamashin hasken rana zuwa samar da wutar lantarki, kasar Sin ta kasance jagora a cikin masana’antar samar da makamashi bisa hasken rana. Sama da shekaru goma da suka gabata, masana’antar makamashin hasken rana ta kasar Sin ta dogara kacokan ga kasashen waje wajen samar da albarkatun kasa da fasaha.

A yau, kididdiga daga kungiyar masana’antun samar da makamashi bisa hasken rana ta kasar Sin ta nuna cewa kamfanonin kasar Sin suna matsayi na daya a harkar samar da abubuwa masu mahimmanci guda hudu wadanda ake sarrafa makamashin hasken rana da su wato polycrystalline silicon, silicon wafers, da baturun cell, da sauran jiga-jigan sarrafawa.

LABARAI MASU NASABA

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Ci gaban da kasar Sin ta samu a masana’antar sarrafa wutar lantarki bisa hasken rana ya nuna aniyar kasar na aiwatar da manufofinta na fitar da karancin sinadarin carbon da kuma magance matsalar sauyin yanayi a duniya. Tun daga shekarar 2022, kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri a sabbin makamashi da suka hada da wutar lantarki mai aiki da hasken rana da kuma karfin iska, wanda ya haifar da raguwar dogaro da albarkatun waje na mai da iskar gas a cikin shekaru 30 da suka gabata.

A cewar hukumar kula da makamashi ta kasar, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2023, karfin makamashin da ake sabuntawa da aka girka a kasar Sin ya zarce kilowatt biliyan 1.3, wanda a karon farko ya zarce karfin da aka girka na makamashin kwal a tarihin kasar Sin. Karfin wutar lantarkin kasar Sin bisa hasken rana da karfin iska, da ruwa, da nau’in makamashi daga wasu halittu yana kan gaba a duniya.
Kamar dai yadda wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping na musamman Ding Xuexiang ya bayyana a yayin taron koli kan harkokin yanayi na duniya da ya gudana a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya kamata dukkan bangarorin su karfafa azama wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi tare.

Yayin da take daukar kwararan matakai don yaki da dumamar yanayi, kasar Sin ta kuma bukaci kasashen duniya da su kiyaye manufofi da ka’idojin da aka gindaya a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da yarjejeniyar Paris, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da samun moriyar juna da samun nasara tare. A yayin da ake fuskantar rikice-rikice a duniya, hadin gwiwa ce kawai mafita.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba
Daga Birnin Sin

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
Daga Birnin Sin

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Next Post
Harin Jirgin Sojin Nijeriya A Kan Taron Maulidi Ya Tayar Da Hankali A Kaduna

Harin Jirgin Sojin Nijeriya A Kan Taron Maulidi Ya Tayar Da Hankali A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

October 30, 2025
Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.