Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Mista Wale Edun, ya ce, naira tiriliyan 13 za a nemo rancensa ne domin cike gurbin naira tiriliyan 48 na kasafin kudin 2025.
Ya shaida hakan ne yayin da ke ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala ganawar majalisar zartarwar tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Abin Da Ake Alfahari Da Su (2): Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)
- Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
An tsara cewa za a samu kudin shiga na naira 34,820,000,000,000 a kasafin 2025 daga cikin naira 47,960,000,000,000, da aka tsara kashewa, lamarin da ke nuni da an samu karin kaso 36.8 daga kasafin 2024.
Gibin kasafin 2025 kamar yadda aka tsara ya kai naira tiriliyan 13,140,000,000,000, kwatankwacin kaso 3.89 na GDP.
Edun ya ce an tsara kasafin ne bisa matakin halin da ake da kuma irin ci gaban da aka samu a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu watanni 18 da suka gabata.
“Ko da za mu kalla daga kasashen waje, mu, kamar gwamnatoci da suke fadin duniya, mun damu da yadda za a samu daurewar ci gaba, kudin shiga zuwa kashewa da rance wannan shi ne daidai, ta samar da yanayin da tattalin arziki zai samun bunkasa.”
Ministan ya ce kamfanoni masu zaman kansu suna da rawar takawa a bangaren zuba jari ta yadda za a samu kyautata ayyukan yi, ci gaban tattalin arziki da kuma yaki da talauci da fatara.
Ya yi bayanin cewa gwamnatin Tinubu ta maida hankali kan tsare-tsaren da za su kyautata kasuwancin man Fetur, musayar canji kudade, kuma kokari ya yi nisa na kyautata farashin wutar lantarki.