Yanzu haka ana gudanar da taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko COP27 a takaice, a wurin shakatawa na Sham El-Sheikh dake kasar Masar, inda shugabannin kasashen duniya za su tattauna kan matsalolin dake hana ruwa gudu game da magance matsalar sauyin yanayi dake ci gaba da addabar sassan duniya ta fannoni daban-daban.
Galibin shugabannin kasashen da suka gabatar da jawabai a taron na wannan karo, sun kara yin kira ne ga kasashe masu karfin tattalin arziki, da su dauki matakai na zahiri maimakon maganar fatar baki da suka saba yi a duk lokacin da aka kira irin wannan taro ko wani dandali mai kama da wannan, domin shawo kan illolin da sauyin yanayin ke haifarwa, kamar zafi da fari da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa dake tafe da mamakon ruwan sama da makamantansu.
Haka kuma sun yi kashedin cewa, lokaci fa yana kurewa, kuma duk wani jan kafa kan wannan batu, babu abin zai haifar illa haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Yanzu haka ana kiyasin cewa, mutane miliyan 700, za su rasa muhallansu a nahiyar Afirka, sakamakon rashin ruwan sha nan da shekarar 2030.
Shi ma babban sakataren MDD Antonio Gutteres, ya shaidawa taron cewa, duniya ta doshi hanyar shiga bala’u na sauyin yanayi, wanda kusan kowa yana ganinsu a sassan duniya, kamar irin matsalolin da aka ambata a sama na ambaliyar ruwa da matsanancin fari da sauransu.
Wani rahoto da hukumar kula da makamashi ta MDD ya nuna cewa, a shekaru 8 dake tafe, ana iya cewa, duniya ta kama hanyar fuskantar zafi mafi tsanani a tarihi.
Shin ina muka dosa? Hukumomin MDD gami da kungiyoyi masu zaman kansu ma, sun yi kashedin cewa, an samu karuwar matsalar karancin abinci mai gina jiki a cikin shirye-shiryen kula da abinci mai gina jiki a fadin yankin kahon Afirka, wannan ma wata alama ce ta matsalar sauyin yanayi, haka kuma mutane da dama sun rasa abubuwansu na rayuwa, da hanyoyin da za su iya magance wannan bala’i, sannan kuma sun dogara baki daya kan taimako don biyan bukatunsu na yau da kullum, matakin da zai iya kalubalantar farfadowar fari.
Yanzu dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Ko dai duniya ta mayar da hankali wajen daukar managartan matakan magance wannan matsala ko kuma duniya ta ci gaba da shiga hali na garari sakamakon matsalar sauyin yanayi.