Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da bunkasuwar tattalin arziki Navid Hanif, ya shedawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, kasar Sin na da dabaru da fasahohi masu kyau a fannin ingiza zamanintarwa da hadin kan kasa da kasa, da sa kaimi ga canja salon makamashi, dukkansu abin koyi ne ga duniya.
A cewarsa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kawar da talauci, raya masana’antu, da yin amfani da sabbin fasahohi, kana tana da gogewa masu tarin yawa, da za ta iya rabawa ga duniya. Zamanantarwa irin na kasar Sin na da matukar amfani ga kasar Sin, kuma sauran kasashe ma za su iya koyo daga gare ta.
Ya kuma yi imanin cewa, akwai bukatar kasashe su koyi kyawawan manufofi da ayyukan juna, yadda kasar Sin ke da kwarewa da kuma musayar gogewarta, zai taimaka wa wasu kasashe wajen zabar salon zamanintarwa da zai dace da yanayin kasashensu da kuma biyan bukatunsu.
A ganin Hanif, Sin tana hadin kai da kasashe mambobin MDD don aiwatar da shawarar raya duniya baki daya, da kafa tawagar sada zumunta wajen aiwatar da shawarar a dandalin majalisar. Ya ce, shawarar raya duniya ta nuna kyakkyawan fata da alkawarin da kasar Sin ta yi wajen inganta ci gaban duniya. (Amina Xu)