Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau kuma za mu kawo muku yadda uwargida za ta gyara gashinta a saukake.
Ga Abubuwan da za a tanada:
Man Shanu, Hular Gashi
Da farko za ki tsefe kanki ki taje shi, sai ki dakko man shanun ki rika tsaga gashin kina shafawa haka za ki yi kamar yadda ake shafa man kitso har ki gama kan gaba daya, sannan sai ki rika shasshafawa jikin gashin sai ki daure gashin, sannan ki dakko wannan hula ki sa ki barshi ya yi kamar awa daya zuwa biyu sai ki wanke za ki ga yadda gashinki zai zama.
Wani Hadin:
Abubuwan da uwargida za ta tanada:
Kwai, madara ta ruwa, zuma, man shanu:
Za ki fasa kwai ki hada da man shanu sai ki zuba madara da zuma akai ki kwaba su, su kwabu sosai su hade jikinsu sai ki shafa a kanki kamar yadda za ki yi na man shanu haka shima za ki yi bayan kin gama ki sa hular gashi ki barshi ya yi kamar shima awa daya zuwa biyu sai ki wanke.