A’uzu billahi minassh shaidanir rajim, Bismillahir rahmanir rahih, Allahummma salli ala sayyidina muhammmdinil fatihi lima uglikk wal katimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki walhadi ila siradikal mustakim wa’ala a’lihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim, waradiyallahu an as’habi rasulallahi SAW, wala haula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim, ya himmatash sheikh ihdiri lana buhazal mahdari wal ta’adifi binazratin ta’ati lana bizzafari.
A cigaba da karatunmu na baya, yau za mu tashi a fasali na Bakwai, wanda zai yi magana a kan Dabi’un Annabi (SAW) kan abubuwan da suka wajabta a al’ada (a rayuwa).
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Horor Da Kasar Sin Take Tallafawa Ya Inganta Yaki Da Nakiyoyin Da Aka Binne A Somaliya
Abubuwan da suka zama dole a rayuwa ko al’ada (in ba a yi su ba, babu rayuwa) Malamai sun kasa su gida Uku.
Gidan farko an raba su kaso biyar, wanda Muradin shari’a, shi ne tabbatar da su da inganta su, in aka inganta su, rayuwar mutum ta lahira da ta duniya za su yi dadi, in aka bata su rayuwar mutum ta lahira da Duniya ba za su yi kyawu ba. Gasu kamar haka:
Kiyaye addini: wanda ya kafa Demokuradiyya, ya bayyana cewa, in aka wulakanta addini, to demokuradiyya ta fadi. Kamar yadda Annabi (SAW) ya fada cewa a Hadisin Jibrilu, addini abu Uku ne – Meye Musulunci Da Imani Da Ihsani, Annabi SAW ya fada.
Kiyaye Rai: Allah ya umurce mu, mu kula da rayukanmu na kanmu, domin dukkanmu rayukanmu ajiyar Allah ce, kuma amana ce ya ba mu a kanmu.
Kiyaye Zurriya: Zuriyarmu amana ce a gare mu, don haka dole ne kiyaye amanar yara (zuriya), saboda auratayya, za a dinga cewa wane dan gidan wane ya auri ‘yar gidan wane, an samu jika a gidan wane. Ba wai mu kasance kamar dabbobi ba, kawai mace ta fita waje ta yo ciki ta dawo gida ana murna ta samu ciki.
Kiyaye hankali: Hankali da oshi ake gudanar da komai, in babu hankali, mutum yana komawa dangin dabbobi, sabda haka, kiyaye hankali ya zama dole.
Kiyaye Dukiya: Dukiya da ita ake shirya harkokin rayuwa na yau da kullum, rayuwa sai da kudi.
Rayuwa tana kewayawa da jujjuyawa a kan wadannan abu biyar da muka lissafa, in aka kiyaye su sai duniya da lahirar mutum ta yi kyau, in kuma aka tozarta su, sai duniya da lahirar mutum ta kuntata.
Ubangiji tabaraka wata’ala ya fada mana yadda ake kiyaye su a fadinsa da cewa:
“Kul ta’alau atlu ma harrama rabbukum alaikum, alla tushriku bihi shai’an, wa bil walidaini ihsana, wala taktuli auladakum kashyata imlak, Nahnu narzukukum wa iyyahum, wala takrabul fawahisha ma zahara min ha wa ma badan, wala taktulun nafsallati harramallahu illa bilhakki, zalikum wassakum bihi la’allakum ta’akilun. Wala takrabu malal yatimi illa billati hiya ahsan hatta yabluga ashuddah, wa’auful kaila wal mizani bil kisdi, wa iza kultum fa’adilu walau kana za bilkurba, wabi’ahdilahi aufu, zalikum wassakum bihi la’allakum tazakkarun, wa’anna haza siradi mustakiman fattabi’uhu, wala tattabi’us subula fatafarraka bikum an sabiliy, zalikum wassakum bihi la’allakum tattakun”
Ya rasulullahi “Ka gaya musu, ku zo in in fada muku abubuwan da aka haramta muku: kar ku hada Allah da komai, ku yi wa iyaye biyayya, kar ku kashe ‘ya’yanku sabida tsoron talauci, ni nake azurta ku da su, kar ku afka wa alfahasha (zina) wacce ta fito fili da wacce ta buya, kar ku kashe ran da aka haramta muku sai dai da gaskiya, wannan ita ce wasiyyar da Ubangiji ke yi muku, ko za ku hankalta. Kar ku kusanci dukiyoyin marayu da zalunci sai dai dukiyar kwadago, har zuwa lokacin da za su mallaki hankalinsu, ku cika mudu da ma’auni iya karfinku, Allah bai dora wa rai abin da ya fi karfinta, idan za ku yi magani ku yi adalci ko a kan dan’uwanku ne, ku cika alkawuranku da Ubangiji, wannan ita ce wasiyyar da Ubangiji ke yi muku, ko za ku wa’azantu. Wannan itace hanyata mikakka (tafarki na), to ku bi ta, kar ku bi bangarori sai ta karkatar da ku daga kan hanyata, wannan ita ce wasiyyata gare ku, ko za ku shiryu.”
Wadannan Larurori biyar da muka lissafa muku a sama su ake kira da ‘maksadush shari’a’, su ne Allah yake bayaninsu a cikin ayar da ta gabata.
· Kiyaye addini: Allah Ubangiji yana cewa “Karku hada shi da komai…”
· Kiyaye Rai: Allah Ubangiji yana cewa “Kar ku kashe ‘ya’yanku…”
· Kiyaye Zuriyya: Allah Ubangiji yana cewa “Kar ku kusanci alfahasha – Zina…”
· Kiyaye Hankali: Allah Ubangiji yana cewa “Ku kiyayi kayan maye…”
· Kiyaye Dukiya: Allah Ubangiji yana cewa “Kar ku kusanci dukiyar marayu da zalunci…”
Sauran hudun su ne:
· Cin abinci: Dan Adam ba zai taba wadata daga cin abinci ba, don ba zai rayu ba, in bai ci abinci ba. Akwai abinci, akwai masu raka abinci, Misali: shinkafa, Masara, Gero Doya, da sauransu amma nama, kifi da sauransu masu raka abinci ne.
· Shan Ruwa: Dan Adam ba zai rayu ba in babu ruwa a rayuwarsa, jininsa sai da ruwa yake gudana.
· Iska: Dan Adam sai da shakar iska zai rayu.
· Matsuguni: Dan Adam yana bukatar kariya daga zafin Rana, Ruwan sama, Sanyi da sauransu.
Wasu daga cikin Larurorin da ba dole ba ne a rayuwar dan Adam amma suna da matukar amfani, sun hada da:
· Haske: Don bukatar larurar dare
· Kayan sawa: Dan Adam ya rufe tsiraicinsa, yana da matukar amfani, kuma dole ne.
· Lafiya: Dan Adam in ba shi da lafiya, dole ya tashi ya nemi lafiya.
· Haihuwa: Dan Adam yana bukatar haihuwa domin ya gina gari, ya tsare gari. Sarkin gari da ke shugabantar mutum 100 ya fi wanda ke shugabantar mutum 50. Yawan jama’a darajar sarki.
· Ilimi: Dan Adam yana bukatar karatu, don ya iya kasuwanci, ya iya mu’amala da sauran kabilu, iya karfinsa.
· Ba-haya: Dan Adam yana bukatar zagayawa, don fitar da kazantar da cikinsa ya tara.
· Aure: Dan Adam yana bukatar aure a rayuwarsa, sabida duk jinin da ke zirga-zirga a jikinsa ya samu sukuni. Masu hikima na cewa “Lafiya na cikin abu Hudu: 1- Amai 2- Gudawa 3- Kaho 4- Aure
· Hutun zuciya: Da yawa Annabi (SAW) yake horo da ayyukan hutun zuciya, yake kuma horo da kin aikata ayyukan harzuka zuciya, sabida dan Adam yana bukatar zuciyarsa ta huta ta samu nutsuwa. Shehu Tijjani Abul Abbas (RA) yana cewa: “Duk wanda bai kiyaye harzuka zuciyar dan Darikata ba, halaka za ta same shi”
· Barci: Dan Adam yana bukatar bacci a rayuwarsa, akwai kwanakin da in dan Adam ya yi bai yi barci ba, zai iya samun tabin hankali.
· Kasabi: Dan Adam yana bukatar abin da zai rike rayuwarsa ta ci gaba, na daga neman abinci da abin da jikinsa ke bukata.
A cikin dukkan wadannan abubuwan da muka lissafa, Malamai sun kara kasafta su zuwa gida Uku.
Kason farko, Falala a cikinsu ana bukatar a karanta; kaso na biyu, falala a cikinsu a yawaita su; kaso na karshe, falala a cikinsu tsakaitawa (wani da yawa, wani karantawa, wani tsakaitawa)
Akwai abubuwa wadanda in kana so ka zama cikakke, al’ada da addini sun so a karanta aikata su, kamar cin abinci da bacci (Sai dai, ya danganta, kowa da irin yadda Allah ya yi shi, to iya karfinka, ba yadda za ka halaka ba).
Sayyidina Aliyu (Karramallahu Wajhahu) yana cewa, duk wanda ya yi bacci har na tsawon Sa’o’i Uku, to ya biya abin da ya wajaba a kanshi. Larabawa da duk masu hikima na daga Malaman falsafa da likitanci, sun tafi a kan cewa, yana da kyau a karanta cin abinci da bacci. Kamar yadda yakan zama zargi ga mutane na kabilu daban-daban a ce “wa ne ya cika cin abinci”. Babu wani da yake alfahari a ce masa ya cika cin abinci.
Amma fa duk da haka, ana nufin karanta cin abinci yadda ba zai illata mutum ba. Domin yawaita cin abinci da shaye-shayen kayayyaki, yana nuni da cewa, mutum yana da zari da handama.