‘Yan Nijeriya masu kasuwanci a Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun yi murna da abin da aka dade ana jira, yayin aka dage haramcin ba su biza zuwa kasar.
A cewar hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa, dawo da ba da bizar zai fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Maris din shekarar 2024, wanda aka ce ya samo asali ne sakamakon tattaunawa tsakanin shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Daular, Sheikh Mohamed bin Zayad Al Nahyan.
An bayyana hakan ne ta wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a ranar Talata.
Idan za a iya tunawa dai kasar ta kakaba wa ‘Yan Nijeriya takunkumin biza sakamakon abubuwan da ba su ji dadin faruwarsu ba a shekarun da suka gabata.
Kafin wannan haramcin dai, kasar ta kasance wurin yawon bude ido ga ‘Yan Nijeriya da karatu da kuma kasuwanci.