Daya daga cikin dattawa a masana’antar Kannywood da suka dade ana damawa dasu a masana’antar tsawon shekaru fiye da 40, Sani Moda, ya yi batutuwa da dama akan wannan sana’a da ya shafe tsawon shekarun kuruciyarshi a cikinta.
Moda, a wata hira da ya yi da rfI Hausa ya nuna tausaya ga matasa da ke tasowa a masana’antar musamman mata, wadanda yace mafi yawancin abinda ke kawo su Kannywood bai wuce Suna, Kudi da daukaka ba.
- Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?
- Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
Duk da cewar na shafe tsawon lokaci a wannan harka amma daga ni bazan bari wani daga cikin zuri’a ta ya yi fim ba, wannan magana ba ina yinta saboda ko ban samu alheri kokuma wani abu a harkar fim ba, illa dai nasan cewar harkar a yanzu ba kamar a shekarun baya ba take.
Manyan mutane kamar su Malam Dan Haki, Karkuzu da irinsu Samanja duka ba su yi fim don kudi ko daukaka ba, kawai abin ne yake burgesu sai kuma isar da sakonnin gwamnatin tarayya ko ta jaha, saboda haka da dama wadanda ke shigowa yanzu suna yi ne saboda wani abu da suke tunanin zasu samu.
Tunda nake zaune a gida ina jinyar ciwon suga har ta kai ga an yanke mani kafa daya, akwai wadanda basu taba kirana ko a waya suka tambayeni yaya jikina ba duk da cewar sun sani bani da lafiya, saboda haka babu wani aibu idan ni ko wani dan fim yace ba zai bari dan da ya haifa ya shiga harkar fim ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp