Jimillar daliban Najeriya 65 ne aka shiryawa wata gagarumar tarba ranar Laraba, bayan dawowrasu kasar, bayan da suka kammala shirin bayar da tallafin karatu a kasar Sin.
Daliban, wanda kamfanin gine-ginen na kasar Sin (CCECC) ya dauki nauyinsu, sun samu gagarumar tarba da jinjina, da jawabai masu sosa zuciya, a yayin wani kasaitaccen biki da aka shirya a babban ofishin kamfanin gine-gine na kasar Sin dake Abuja, babban birnin Najeriya.
Manufar shirin bayar da tallafin karatun wanda gwamnatin Najeriya da hukumar CCECC da jami’o’in kasar Sin guda biyu suka shirya, ita ce inganta mu’amalar ilimi, da kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
Da take jawabi a yayin bikin, babbar sakatariyar ma’aikatar sufurin Najeriya, Magdalene Ajani, ta yi fatan wadanda suka kammala karatun, za su taka rawar da ta dace a kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi a halin yanzu na inganta harkar sufuri, musamman bangaren layin dogo. (Ibrahim Yaya)