Likitoci masana lafiyar kananan yara sun bayyana cewa, fitar da hakorin da yara suke yi ko kadan baya kawo gudawa ko amai kai-tsaye. Sai dai, mafi yawan al’umma na alakanta wasu abubuwa da ke faruwa lokacin fitar hakoran a matsayin musabbabin gudawa da aman da ke faruwa a daidai wannan lokaci.
Wadannan abubuwa kuwa sun hada da:
1- Lokacin da yaro ke fara fitar da hakori, ya yi daidai da lokacin da ake fara bashi abincin gida (supplementary feeding), wanda rashin sabo da abincin kan iya bata masa ciki har ya sanya shi gudawa ko amai nan take. Cikin yaro kan dauki lokaci kafin ya saba da irin abincin da za a fara ba shi, musamman idan ya shafe wata shida ba ya shan komai sai mama.
2- Lokacin fara fitar hakori ya yi daidai da lokacin da yaro zai fara rasa sojojin garkuwar jikin da yake samu daga mahaifiyarsa a lokacin da ta haife shi. Rasa Wadannan sojojin garkuwar jiki, kan raunana garkuwar jikinsa na dan wani lokaci kafin tasa garkuwar jikin ta yi karfi. Wannan raunin kan sa ‘yan cututtuka kadan su sanya yaro gudawa, amai, zazzabi ko kuma zafin jiki.
Watakila mai karatu zai yi mamaki, idan aka ce garkuwar jikin jariri sabon haihuwa ta fi ta dan wata shida karfi, wannan ba abin mamaki ba ne; saboda idan aka haifi yaro akwai sashen wasu sojojin garkuwar jikin mahaifiyasa da za su biyo shi su taimaka masa, domin fada da cututtuka. Wadannan sojojin ba sa iya wuce wata shida suna aiki a jikin yaro, daga nan kuma za su mutu su bar yaro da garkuwar jikinsa matashiya.
3- A lokacin fitar da hakora, dasashin yaro ya kan dan yi kumburi ya fara kaikayi da ciwo a wajen da hakoran za su fito, wannan shi zai sa yaro ya kama sanya hannu a baki da kuma duk abin da ya samu; sai ya sa a cikin bakin nasa, domin ya ji saukin wannan kaikayi da ciwo da suke damun sa. Sanya abubuwa da dama wadanda ba a tsafta ce ba a cikin baki, kan sanya yaro kamuwa da kananan cututtukan da za su haifar masa da amai da kuma gudawa. Bugu da kari, garkuwar jikin yaro a wannan lokaci na fuskantar barazana; kamar yadda muka yi bayani a baya, saboda haka; ba za ta iya yin fada da kananan cututtukan ba.
4- A lokacin fitar da hakora, a kan samu karin fitar da yawu da kuma wasu sinadaran ‘cytokines’ daga cikin jikin yaro. Wannan shi kadai ya kan iya yin sanadiyyar tsinkewar bahayar yaro.