Daga cikin jihohi 36 na kasar nan, jihohi biyar ne kacal, suka samu nasarar samo masu zuba hannun jari a zango na uku na shekarar 2024.
Hakan na kunshe ne, a cikin wani rahoton cibiya ta kasa, da ke kula da shigo da kaya cikin kasar nan wato NCI da ta fitar na zangon na uku na shekarar 2024.
- Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
- Yayin Da Ake Gab Da Bukukuwan Kirsimeti: ‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Rayuwa Cikin Matsin Tattalin Arziki
Daukacin wadannan jihohin biyar, sun samo masu zuba hannun jari da ya kai na dala biliyan 1.25, wanada ya hada da zuba hanun jari daga kasar wajem da kuma na cikin gida.
Hakan ya nuna cewa, masu zuba hanun jarin, sun fara nuna kwarin guiwar da suka da shi, ga tattalin azrikin kasar nan.
Jihar Legas ta samu zuba hannun jarin da ya kai na dala miliyan650.42, sai kuma Abuja, da samu zuba hannun jarin da ya kai na miliyan 600, inda kuma jihar Kaduna, ta samu dala miliyan 1.95.
Sauran jihohin sune; Enugu da samu dala miliyan 184,229, inda kuma jihar Ekiti, ta samu zuba hanun jarin da ya kai na dala miliyan 96,600.
Wasu daga cikin jihohin sun hada da; Bayelsa, Ebonyi, Gombe, Jigawa, Kebbi, Taraba, Yobe, da Zamfara, wadanda suka samu masu zuba hannun jari daga ketare, a cikin shekaru shida da suka gabata.