Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa, daukar jami’an ’yan banga 7,000 a jihar zai taimaka wajen rage karancin jami’ai don magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da shirin horas da jami’an ‘yanbanga 7,000 a kwalejin ‘yansanda ta Kaduna a ranar Asabar.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, an zabo wadanda za a horas ne daga dukkan kananan hukumomin jihar Kaduna, kuma wannan babban mataki ne na cika alkawarin da muka dauka ga al’ummar jihar Kaduna.
“A cikin tsare-tsaren gwamnatinmu, mun himmatu wajen karfafa ayyukan jami’an ‘yanbanga (KADVS). Tun lokacin da aka kafa ta, KADVS tana aiki tare da hukumomin tsaro don yaki da masu aikata laifuka.
“Amma KADVS tana fuskantar kalubale na rashin isassun jami’ai don samun nasarar yaki da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka. Don haka, gwamnatinmu ta yanke shawarar daukar jami’a 7,000 aiki a ma’aikatar tsaro ta Kaduna (KADVS).
A cewarsa, daukar jami’an da tantance wadanda za a horas, na daga cikin kokari da hadin guiwa da aka samu a tsakanin shugabannin kananan hukumominmu, da shugabannin gargajiya da malam addini.