Dan wasan gaban Manchester United da ke zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa, Marcus Rashford ya na ganin da wuya ya sake buga wa Manchester United wasa karkashin jagorancin kocin kungiyar na yanzu Ruben Amorim, duk da kuma yace ba za a yi gaggawar yanke shawara ba.
Rashford ya ci kwallo ta hudu tun bayan komawarshi Aston Villa a matsayin aro a watan Fabrairu yayin da suka sha kashi a hannun Manchester City da ci 2-1 ranar Talata, zaman aron dan wasan a Villa Park zai kare ne a karshen kakar wasa ta bana.
- Ba ‘Yan Nijeriya Ne Ke Kai Mana Hare-hare A Benuwai Ba – Gwamna Alia
- Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Amma yayin da kwantiraginsa na United zai ci gaba har zuwa shekarar 2028, majiyoyin da ke kusa da dan wasan sun tabbatar da babu wani abu da ke nuna tabbacin komawar Rashford Old Trafford, Amorim ya ajiye Rashford daga tawagarsa tun farko a watan Disamba, hakan na nufin United za ta yanke shawarar ko za ta sayar da dan wasan mai shekara 27 ko kuma ta bar shi ya cigaba da zaman aro a Villa.
Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp