A kwanakin baya aka samu jarumar fina finan Hausa na Kannywood Amal Umar da laifin baiwa jami’in dan sanda cin hanci domin ya dakatar da wani bincike da yake yi a kan wani mutum da ake kyautata zaton saurayinta ne.
An zargi Amal wadda saurayin nata ya yi ikirarin tura mata wani kaso daga cikin kudin da ake shari’a akansu da laifin yunkurin bayar da cin hanci ga wani jami’in dan sanda domin dakatar da bincike a kan saurayinta da ake zargi da sama da fadi da wasu makudan kudade.
- Hajjin Bana: Karin Naira Miliyan 1.9 Ya Jefa Dubban Maniyyata Cikin Garari
- Makasudin Gayyata Ta Da Jami’an Tsaro Suka Yi Kan ‘Yan Bindiga – Sheikh Gumi
Jarumar ta Kannywood ta gurfana a gaban kotun majistare mai lamba 24 dake unguwar Gyadi-Gyadi a cikin birnin Kano bisa zargin yunkurin ba wa jami’in tsaro cin hanci.
Ana zargin jarumar da yunkurin ba da cin hancin kudi har Naira 250,000 ga wani jami’in ‘yansanda mai suna ASP Salisu Bujama na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, hedikwatar shiyya ta daya a Jihar Kano.
A cewar mai gabatar da kara, Amal ta bayar da cin hancin ne da nufin a dakatar da binciken ‘yansanda kan zargin karkatar da kudade da saurayin jarumar, mai suna Ramadan Inuwa yayi a wata harka ta kasuwanci.
Laifin da ake zargin jarumar ta Kannywood da aikatawa ya sabawa sashe na 118 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta bayarwa da karbar cin hanci ga dan sanda.
Zuwa yanzu dai ana dakon hukuncin alkalin kotun majistare mai lamba 24 dake unguwar Gyadi Gyadi da ke Kano zai yanke a kan jarumar idan aka sameta da laifi ko akasin haka.