- el-Rufa’I Ya Taba Fada: Zan Iya Rantsewa Da Alkur’ani Ban Saci Ko Kobo Ba, Aiki Na Yi Da Shi
- Al’umma Na Bukatar Bayani Don Da Uba Sani Aka Yi Komai – Kakakin Dattawan Arewa
- Ya Kamata A Kafa Kwamitin Bincike – Shehu Sani
Biyo bayan kalaman da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi na cewa, ya gaji bashin miliyoyin Dala da biliyoyin Naira daga gwamnatin Nasir el-Rufai da ya karbi ragama a hannunta; fagen siyasar jihar na ci gaba dumama sakamakon kurar da ke tashi.
A yayin gudanar da wani taro da al’ummar jiha kwanan nan a zauren taro na Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Dandalin Murtala Sikwaya, Uba Sani, ya ce ya gaji bashin da kimanin Dala miliyan 587 da Naira biliyan 85 da kuma tarin ayyukan da ba a kammala ba daga Gwamnatin Nasir el-Rufai. Sai kuma ayyuka 115 wanda ‘yan kwangila ba su kammala ba.
- Masanin Dokokin Kasa Da Kasa Na Birtaniya: Sin Tana Da Ikon Mallakar Tsibiran Yankin Kudancin Tekun Sin
- Wani Dansanda Mai Rakiyar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Rasu Acikin Jirgin
Haka zalika, Uba Sani ya ce sakamakon dimbin bashin, hatta albashin ma’aikata ba zai iya biya ba. Kodayake, tuni ya kai kukansa wurin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan yadda zai taimaka masa wajen warware wannan matsala, amma sai shugaban kasar ya bayyana masa cewa; shi ma abin ya fi karfinsa, sakamakon an ciyo bashin ne daga Bankin Duniya.
Haka kuma Gwamna Sani ya koka kan yadda farashin canji ya tashi, wanda ya sa yanzu Jihar Kaduna na biyan kusan ninki uku na bashin.
Ya bayyana cewa an cire naira biliyan 7 daga cikin biliyan 10 da gwamnatin tarayya ta ware wa jihar a watan Maris sakamakon biyan bashi.
A cewar gwamnan, an bar jihar da naira biliyan 3 wanda ba za su isa biyan albashin ma’aikata ba, saboda a duk wata jihar na biyan albashin ma’aikata naira biliyan 5.2, wanda ba za ta iya ba har sai an ci bashi.
Ya ce ya tamabaya kan wannan kudade da aka cire ko na wannan watan ne kadai, sai aka ce a’a, za a iya kai shekara 6 ana cirewa. Gwamna Sani ya ce ya zabtare albashin kwamishinoni da alawus-alawus da kusan naira miliyan daya,haka kuma ya ce ya cire wa mataimakasa na musamman albashin da ya kai naira 400,000, sannan kuma gwamnati ba za ta iya sayen mota ba saboda rashin kudi, wanda hatta shi kansa gwamna da mataimakiyarsa ba su samu sabuwar mota ba, domin a rage kudaden da ake kashewa.
Ko shakka babu, wadannan kalamai sun yi matukar jawo hankali tare da muhawara yadda ya kamata, musamman ga al’ummar jihar; wadanda ke kallon al’amarin a matsayin wani sabon abu, wasu kuma ke ganin cewa; tuni sun yi hasashen faruwar hakan, domin kuwa irin wannan abu ba sabo ba ne a siyasar wannan kasa. Misali, irin hakan ta faru a Jihar Kano tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Jihar Gombe tsakanin danjuma Goje da dankwambo da kuma Jihar Zamfara tsakanin Sani Yariman Bakura da Mamuda Dallatun Shinkafi da sauran makamantansu.
Tuni dai wasu makusantan tsohon Gwamna el-Rufai, ciki har da daya daga cikin ‘ya’yansa da tsofaffin jami’an gwamnatinsa, suka fara mayar da martani a kan wannan lafazi da gwamnan ya yi, lamarin da yanzu ya fara sauya salon siyasar jihar baki daya. Har ila yau, wannan rikici da ya fara kunno kai; ya jefa Jam’iyyar APC mai mulki a Kaduna cikin rudani, wanda ya yi sanadiyyar su kansu Talakawan jihar; fara tofa albarkacin bakinsu.
Hakan ya sa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar, suke zargin gwamnan da cin amanar tsohon gwamnan, ta hanyar yi masa butulci.
Zuwa yanzu dai, mafiya yawan masu rike da madafun iko a jihar, cikinsu ya duri ruwa; domin kuwa a nasu lissafin da hasashen wannan rikici, zai iya raba su da mukamansu.
Musamman ganin yadda rikicin ya cinye kujerar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a jihar, Hajiya Maryam Suleiman Mai Rusau.
Mai Rusau dai, ta zagi Gwamna Uba Sani da rashin yin katabus, tun bayan lokacin da ya dare karagar kujerar wannan mulki ta Jihar Kaduna.
A wani sako da ta wallafa a shafukan sada zumunta ta bayyana cewa, “Kuka bayan hari kake yi gwamna, za ka ce ba ka san da bashin ba ne a lokacin da kake neman gwamnan ido rufe, ka hana kowa zama, kai ne can kai ne nan; sai yanzu da ka zama gwamna?”.
“Yanzu ka zama kuma kana neman dora wa tsohon gwamna laifi, ai da ba ka nemi kujerar gwamnan ba; saboda haka, idan ba za ka iya ba yanzu, ka sauka mana kawai,” in ji ta. Ana ganin kashi 70 cikin 100 na masu rike da mukaman siyasa cikin Gwamnatin Uba Sani, mukarraban el-Rufai ne; wanda wasu ke ganin idan har rikicin ya ci gaba, suna iya rasa mukamansu.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna tsohon gwamnan na Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai yana cewa, ko kadan bai saci dukiyar al’ummar jihar ba tsawon zango biyun da ya kwashe yana mulki a jihar, a cewar tasa; gida daya tak ya mallaka kafin ya kai ga zama gwamnan a unguwar Sarki da ke Kaduna.
“Zan iya rantsewa da Allah ban taba satar kobo a asusun gwamnati ba, sannan kuma ina kalubalantar duk wadanda suka mulkin jihar, da su ma su fito su rantse da Alkur’ani cewa; a lokacin da suka yi nasu mulki, ba su saci ko kwabo na al’ummar jihar ba,” in ji el-Rufai.
A zantawarsa da wakilinmu, Kakakin kungiyar Dattawan Arewa (Arewa Elders Forum), Abdul’azez Suleiman ya bayyana cewa, tasirin dimbin basussukan da tsohon gwamnan ya bari, na da matukar muni da za su iya kawo illa ga ryuwar al’ummar jihar na tsawon lokaci. “Wannan matsala ce da za ta yi wuya a iya kayyade tsawon lokacin da jihar za ta dauka wadannan basussuka na bin ta, ba tare da samun cikakken bayani kan hanyoyin samun kudaden shiga na jihar a halin yanzu ba da kuma ka’idodin biyan bashin da jadawalin biyansa. Duk da haka, bisa kididdiga; idan jihar za ta ware wani kaso mai tsoka na kasafin kudinta na shekara, don biyan bashi; za ta iya daukar shekaru da daman gaske kafin ta kammala biya”.
“Bashin da Gwamna Sani ya ce ya gada, ya yi matukar haifar da damuwa game da yadda ake tafka barna a harkokin kudi na jihar da kuma yadda aka rika karbar bashi a gwamnatin da ta gabata. Irin wannan dimbin basussuka, ba wai kawai yana hana gwamnati damar samar da muhimman ayyukan more rayuwa ba ne kawai, yana kuma haifar da wani gagarumin nauyi na bashi ga al’ummar wannan jiha baki-daya.”
Suleiman ya kara da cewa, “Ba za a taba mantawa da yadda Uba Sani ya taka rawa, wajen sama wa el-Rufai rancen wadannan kudade ba, a lokacin zamansa a Majalisar Dattawa. Don haka, yana da kyau Uba Sani ya tuno da irin wannan rawa da ya taka wajen bai wa el-Rufa’in wannan dama ta karbar bashi. Sannan, ya tuna lokacin da el-Rufain ya yi ta babatu kawai don wasu daga cikin ‘yan majalisa sun hana shi samun damar karbo wannan bashi, da har sai da ya yi sanadiyyar hana su sake komawa majalisar. Kana Uba Sani, yana sane da yadda el-Rufai ya tabbatar da ganin ya zama dan majalisar dokoki, domin kawai ya samu damar share masa hanyoyin karbar wannan bashi.
Abdulazez ya ci gaba da cewa, “Ya san duk yadda aka yi aka karbo wadannan kudade tare da abin da aka yi da su. Don haka, mu a namu ganin kamar raina mana hankali ake so a yi yanzu, wai yanzu Uba Sani ne ke kokarin wanke kansa daga abin da aka aikata, saboda ya san da ita, sannan kuma da shi aka kulla ta”.
“Saboda haka, dole ne al’ummar Jihar Kaduna ta bukaci cikakken bayani daga wurin dukkannin wadanda suka taka rawa wajen bayar da damar aikata wannan mummunar badakala, ciki kuwa har da Uba Sani,” a cewar tasa.
Haka zalika, Sanata Shehu Sani, tsohon dan Majalisar Dattawa, wanda aka yi ta kai ruwa rana da shi da tsohon gwamna elRufai, sakamakon kin amincewa da ya yi a kan batun ciyo bashin, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa kujerarsa ta Sanata a karo na biyu, ya shaida wa wakilinmu cewa, da ma ya san hakan za ta faru; ganin yadda bashin zai yi mummunan tasiri, musamman a irin wannan lokaci da ake ciki.
Kazalika, Sanatan ya bayyana cewa ba wani abin mamaki ba ne, don an fara kai ruwa rana atsakanin Uba da el-Rufai.
“Na yi matukar godiya ga Allah da babu hannuna cikin karbo wannan bashi, sannan yanzu mutane za su fahimci dalilin da ya sa muka ki amincewa a karbo bashin a wancan lokaci.
Don haka, muna kira da a kafa kwamitin bincike a kan yadda el-Rufai ya kashe wadannan makudan kudade na dala da na Naira a wannan jiha da sunan aiki,” in ji Shehu Sani.
Mafi yawan mutanen da wakilinmu ya zanta da su, sun bayyana cewa, ko kadan ba sa goyon bayan wannan rikici, dalili kuwa shi ne; zai iya dakile ci gaban jihar ta bangarori da dama, inda suka ce duk jihar da ake samun irin wannan takun saka tsakanin tsohon gwamna da sabo, ba a fiya samun ci gaba na a zo a gani ba.
Wani magidanci, mai suna Muhamadu Abdullahi a jihar ta Kaduna ya bayyana cewa, duk mai kishin ci gaban Jihar Kaduna, ba ya goyon bayan wannan rikici; saboda zai iya dakile shirin ci gaban al’umma, musamman talakawa. “Maganar gaskiya, mu al’ummar Jihar Kaduna ba ma goyon bayan wannan rikici, domin kuwa a karshe mu ne abin zai fi shafa”.
Haka nan, ita ma Hajiya Sayyada Abdullahi Mai Gurasa, ta ce, su babu ruwansu da wani rikicin Uba Sani da el-Rufai, babban abin da suke bukata shi ne; samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar Jihar Kaduna baki daya.
“Wallahi ni a nawa hasashen, gani nake wannan rikicin kamar shirya shi aka yi, don kawai a kawar da hankulan Talakawan Jihar Kaduna, idan ba haka kuwa ba; ai shi Gwamna Uba Sani, ya san lokacin da ya ba da dama aka karbo wannan bashin, sannan kuma ya san adadin shekaru nawa za a yi ana biya; amma kawai sai yanzu rana tsaka zai ce ga zance ga magana. Abin da ya dame mu yanzu mu a Jihar Kaduna shi ne, yadda za a samar da tsaro da ilimi tare kuma da saukaka mana rayuwa ta yadda mazajenmu za samu saukin rayuwa” a cewarta.
…Rikicin Ya Raba Kan Jam’iyyun Adawa A Jihar
An samu rarrabuwar kawunan a tsakanin gamayyar jam’iyyun jihar goma sha takwas, (Inter Party Adbisory Council Of Nigeria) kan alkiblar da ya kamata su fuskanta a batun bashin da Gwamna Uba Sani ya kwarmata.
A wani taron manema labarai da shugaban na IPAC Alhaji Tijjani Mustapha ya jagoranta, an tashi baranbaran; inda wasu mambobin kungiyar suke zargin shugaban da karbar makudan kudade daga fadar gwamnatin jihar da zimmar kare furucin Gwamna Uba Sani, a kan el-Rufai tare da goya wa gwamnatin baya wajen yada manufofinta.
Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na sakatariyar cibiyar wakilan kafafen yada labarai ta Jihar Kaduna, an ba wa hammata iska tsakanin wakilin jam’iyyar NNPP Aliyu
Haruna Chakis da kuma shugaban kungiyar da wasu mambobin kungiyar lamarin da ya kai har sai da aka fitar da su da kyar daga dakin taron.
Chakis ya shaida wa manema labarai cewa, ba za a yi amfani da shi wajen yaudarar sauran mambobin kungiyar ba.
“Ba za mu amince da wani ya je ya karbo kudi daga fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, da sunan kare gwamnati ba; saboda mu goma sha takwas ne muke wakiltar jam’iyyu dabandaban, amma sai muka samu labarin cewa wasu mutum biyu sun gana da gwamna a kan rikicinsa da el-Rufai sai yau kuma aka turo mana da sakon cewa; wai ana gayyatarmu taron manema labarai”, in ji shi.
“Wallahi idan na ci gaba da zama a cikin dakin taron nan, Zan wanka wa wani mari ko na fasa kyamarar daukar hoto.
Mu ba mu amince da abin da shugaban wannan kungiya zai karanta wa manema labarai ba.
Don hka, dole ne ya fada mana nawa gwamnati ta ba shi, domin ya kare ta? Ba mu amince a yi amfani da mu wajen yaudarar sauran mambobin wannan kungiya ba”.”Saboda haka, muna so shugaban wannan kungiya ya fito ya fada mana, nawa aka ba shi; ba wai ya ce mana wai shi ne da kudinsa yake daukar nauyin wannan taro na manema labarai ba”, a cewar ta Chakis, wanda tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ne, da ya wakilci mazabar Kawo.
Jim kadan bayan fitar da wakilin Jamiyyar NNPP da wasu magoya bayansa, Shugaban IPAC Alhaji Tijjani Mustapha, ya dauki lokaci mai tsawo yana kare Gwamnati Uba Sani, kan yawan tarin bashin da el-Rufai ya bar mata, inda ya bayyana cewa, a shirye suke wajen su ba shi dukkannin goyon bayan da ya dace.