Dan wasan Damben Boxing dan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, ya saka karfin damtse wajen doke abokin karawarsa, Francis Ngannou, a zagaye na biyu na wasan damben da suka buga a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Joshua mai shekaru 34 ya baje zakaran gasar damben UFC a kasa har sau biyu a zagayen farko da na biyu na wasan wanda ya ja hankalin masu sha’awar kallon damben turawa.
- An Kammala Wasan Karshen Damben Warriors Na Wannan Shekarar A Kano
- Dambe: An Fafata Tsakanin Dan Aliyu Da Rabe Shagon Ebola
Da wannan nasarar ta Joshua ita ce ta 4 cikin nasarorin da ya samu cikin watanni 11, yayin da yake neman dawo da kambunsa na gwarzon Duniya a fagen damben Boxing wanda ya taba rikawa a baya.
Joshua da Ngannou dukkansu bakaken fata ne, inda Anthony Joshua yake da tsatso a Nijeriya, shi kuma Francis Ngannou dan asalin kasar Kamaru ne kuma dukkansu sun lashe manyan kambunan wasan dambe kafin su hadu da junansu.