A watan Janairu na shekarar 1969, Xi Jinping, wanda bai kai shekaru 16 da haihuwa ba a lokacin, ya zo kauyen Liangjiahe da ke arewacin lardin Shaanxi daga birnin Beijing. Ya ce, “Duk inda na je, zan kasance dan asalin tudun Loess.” Shekaru da yawa bayan haka, ya bayyana a cikin wata kasida cewa, “A matsayina na ma’aikacin gwamnati, yankin arewacin Shaanxi shi ne asalina, saboda wurin ne ya dasa mani imanina wanda ba zai canza ba wato yin abubuwa masu alfanu ga mutane a aikace!” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)