Wani mai suna Hamidu Mukhtari, da ake zargin dan bangar siyasa ne, ya yi wa wani dan jarida mai suna Ibrahim Mista Ali dukan tsiya a gidan gwamnatin jihar Adamawa.
Hamidu wnada aka fi sani da Dogo an ce ya yi wa Ali dukan ne saboda sukar da ya yi wa gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri.
- Shugaban Benin Patrice Talon Ya Sauka Beijing
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Alkawarin Ci Gaba Da Yakar ‘Yan Bindiga
Ali ya gamu da fushin Dogo ne a lokacin taron manema labarai da sakataren gwamnatin jihar Awwal Tukur ya hada.
Bugu da kari, ba dai tun yau ba ne Dogo ke yi wa Ali barazana a kan wallafa labaru marasa kyau a kan gwamnatin Umaru Fintiri ba.
Ali ya bayyna cewa, Dogo ya mare shi ya kuma shake shi a gaban jami’an tsaron fadar gidan gwamnatin jihar wadanda daga bisani suka shiga tsakani sannan ya kyale ni.
Kazalika, Dogo dai an ce ya yi kaurin suna wajen cin zarafin duk wanda yake ganin makiyi ne ga gwamnan jihar.
Bugu da kari, a yanzu haka Dogo na da tuhuma a gaban hukumar NDLEA wanda aka bayar da belinsa a 2021 bayan an kama shi da tabar wiwi mai dimbin yawa gidansa
Kwamandan NDLEA na jihar, Muhammed Bello ya tabatar da wannan maganar, inda ya kara da cewa, an kama Dogo ne dauke da tabar wiwi da nauyin ta ya kai kilogiram 166 kuma za a gabatar da shi a gaban kotu.
Har ila yau, Dogo an zarge shi da hannu wajen sace wa da cin zarafin babban jami’in DSS Halilu Musa da kuma cin zarafin kwamishinan INEC, Farfesa Zuru a lokacin sake yin zaben gwamnan jihar zagaye na biyu a watan Afiliu, wanda hakan ya haifar da hatsaniya a jihar.
An tuntubi sakataren yada labarai na gwamnan jihar Humwashi Wonosiko, kan maganar amma bai ce uffan ba, inda ya bayyana cewa, rikicin tsakanin Dogo da Ali bai shafi gwamnatin jihar ba.