An nada Dabide Ancelotti, dan gidan tsohon kocin Real Madrid kuma kocin babbar tawagar kasar Brazil Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin Botafogo, in ji kulob din na birnin Rio de Janeiro, Ancelotti, mai shekaru 35, ya shirya fara aikin horarwa na farko bayan ya zama mataimakin mahaifinsa a kungiyoyin Real Madrid, Eberton, Napoli da Bayern Munich.
Zai maye gurbin Renato Paiba wanda aka kora bayan Botafogo ta fice a zagayen 16 na gasar cin kofin duniya, Dabide Ancelotti ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa karshen shekarar 2026, ya koma kasar Brazil domin kasancewa cikin masu horar da ‘yan wasan kasar Brazil tare da mahaifinsa, amma an sauke shi daga matsayinsa don ba shi damar karbar ragamar horar da Botafogo.
- NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya
- Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa
Carlo Ancelotti ya bar Real Madrid ne a karshen kakar wasa ta bara bayan an nada shi kocin Brazil a ranar 12 ga watan Mayu. Shi ne dan kasar waje na farko da ya jagoranci kasar mai tarihin lashe gasar cin kofin duniya sau biyar tun a shekarar 1965.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp