Shahararren dan wasan Nigeriya, Bictor Osimhen ya zama dan wasa daga nahiyar Afirka na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga a gasar Siriya A ta kasar Italy.
Dan wasan, mai shekaru 26 wanda yake buga wasa a kungiyar Napoli ya zura kwallaye 26 a kakar wasan da aka kammala a kasar.
- Wakilin Sin A Taron Vienna Ya Soki Lamirin Yarjejeniyar AUKUS
- Hukumar GEIDCO Ta Zayyana Ayyuka Da Za A Samar A Afirka
Osimhen ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Siriya a karon farko cikin shekaru 30 kuma yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwar su take haska wa a yanzu.
Har ila yau, dan wasan ya kasance gwarzon dan wasan Siriya A a wannan kakar.
Tuni kungiyoyin Manchester United da Chelsea da Real Madrid suka fara zawarcin dan wasan wanda ake ganin zai iya komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin nahiyar turai.