Dan takarar Sanatan Bauchi ta Kudu, Alhaji Shehu Buba ya kayar da Sanata mai ci, Sanata Lawan Yahaya Gumau na jam’iyyar NNPP a zaben Sanatan da aka gudanar a ranar Asabar.
Kazalika, Bubu ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Garba Dahiru da kuri’u marasa yawa.
- INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Sanatan Zamfara Ta Tsakiya Bai Kammala Ba
- Tinubu Ya Yi Nasara A Jihar Zamfara, Ya Kayar Da Atiku, Kwankwaso Da Obi
Da ya ke bayyana sakamakon zaben a daren ranar Litinin, baturen tattara sakamakon zaben Sanatan, Farfesa Ibrahim Hassan na Jami’ar ATBU da ke Bauchi, ya bayyana cewar dan takarar APC, Shehu Buba ya samu kuri’u 170,505, inda ya kada abokin takararsa na PDP, Garba Dahiru, wanda ya samu kuri’u 165,727.
Shi kuma Lawan Yahaya Gumau, ya samu kuri’u 53,739.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp