• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dangantakar Kasar Sin Da Taiwan, Tamkar Ta Uba Ne Da Dansa

by CMG Hausa
3 years ago
Taiwan

Wasu mutane na kokarin kwatanta rikicin Ukraine da Rasha da batun yankin Taiwan na kasar Sin. Amma abun da mutane da yawa ba su fahimta ba, batutuwan biyu sun sha bambam da juna.

Ukraine ’yantacciyar kasa ce mai cin gashin kanta a yanzu haka, haka ma kasar Rasha, don haka, rikicin dake tsakaninsu, rikici ne na kasashe makwabta, yayin da Taiwan tun fi azal, ke kasancewa wani yanki na kasar Sin dake karkashin ikonta.

  • Yawan Musayar Kudaden Da Aka Adana Na Sin A Karshen Watan Yuli Ya Kai Dalar Tiriliyan 3.1041

Yayin da rikicin Rasha da Ukraine ke mayar da hankali kan tsarin tsaro a nahiyar Turai, batun Taiwan ya shafi cikin gidan kasar Sin ne.

Misali, kamar uba ne da ’ya’yansa, sai wani daga can waje ya ce zai jagoranci yadda ya kamata magidanci ya tarbiyantar ko tafiyar da harkokin ’ya’yansa.

A ganina, babu wani uba da ya san ciwon kansa, da zai bari ana tsoma baki cikin harkokin cikin gidansa ko kuma a nemi nuna masa fin karfin kana abun da yake mallakinsa.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Tun asali, Taiwan ba kasa ba ce, yanki ne a cikin kasar Sin, don haka, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ce ke wakiltar ta a matakin kasa da kasa.

Ban da wannan, atisayen da sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin ke yi a tekun kudancin kasar, ba matakan soji na yaki ba ne, tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, tare kuma da bayyana karfin kasar Sin na dakile duk wata barazana dake neman ta da rikici a yankunanta ko kawo cikas ga kwanciyar hankalin daukacin kasar.

Don haka, duk wani mataki da kasar ta dauka dangane da batun, ta dauke shi ne bisa doron doka, kamar yadda hakkin tsawatarwa ya rataya a kan uba, haka ya kamata kasar Sin ta tsawatarwa Taiwan har ma da masu goya masa baya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Abin Takaici Ne Matuka —Abdullahi Adamu

Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Abin Takaici Ne Matuka —Abdullahi Adamu

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.