Kamfanin Siminti na Dangote ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar samar da gidaje da su yi la’akari da tsarin samar da gidaje ga ‘yan Nijeriya da ya dace da daidai kasafin kudin masu karamin karfi.
Da yake jawabi a wajen bikin baje kolin gidaje na kasa da kasa na Afirka, Daraktan tallace-tallace na Kamfanin Siminti na Dangote, Dolapo Alli, ya ce: “Maganin matsalolin gidaje na bukatar hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, da suka hada da hukumomin gwamnati, masu zaman kansu, da al’ummomi. Gwamnati za ta iya rungumar tsarin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu don samar da gidaje masu rahusa ga al’umma wanda aka fi sani da shirin PPP.
- Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
- Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC
“Ta hanyar tsarin PPP, gwamnati na iya ƙaddamar da gina sabbin gidaje, yayin da kamfanoni masu zaman kansu dake masana’antar gine-gine kuma a saukake musu haraji tare da basu lamuni don saukake samar da kudade na sababbin gidaje masu rahusa.”
Mista Alli, wanda yake jawabi a rana ta musamman ta kamfanin, ya ce, samar da gidaje masu yawa na daya daga cikin dabaru da dama da ake amfani da su wajen magance kalubalen karancin gidaje ga jama’a, inda ya kara da cewa, amma wannan tsarin ya taimaka wajen magance matsalolin da ke tattare da saurin bunkasar birane a kasashe da dama na duniya.
Ya yabawa kokarin Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da shirye-shiryen samar da gidaje masu yawa, inda ya kara da cewa, amma akwai bukatar a cike gibi.
Ya ce: “Nijeriya, ta hanyar shirin sabunta fata na samar da gidaje da gwamnatin shugaba Tinubu ta kirkiro, ta dauki matakan yabawa wajen magance babban gibin da ke tattare da samun lamunin kudade wajen samar da gidaje masu rahusa. Wannan shiri na nuni da cewa, an himmatu wajen ganin ‘yan kasa sun samu saukin mallakar gidaje, musamman masu karamin karfi da matsakaita tattalin arziki.
Ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su aiwatar da ingantattun tsare-tsare tare da samar da filayen gina gidaje masu tarin yawa a Nijeriya.
Kamfanin Siminti na Dangote na daya daga cikin masu daukar nauyin shirin baje kolin gidaje na Afirka (AIHS) wanda za a rufe ranar Juma’a 1 ga Agusta, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp