Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke
Assalamu alaikum wa rahmtullah. Tsira da aminci su tabata ga shugaban halitta, wanda ya zama rahama da jin kai ga dukkan halittar Allah, Annabi Muhammadu (SAW) da iyalan gidansa da sahabbansa (Radiyallahu anhum).
- Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
- Shenzhou-20: Kasar Sin Ta Aike Da ‘Yan Sama Jannati 3 Zuwa Sararin Samaniya
Masu karatu, a wannan makon ma za mu ci gaba da kawo muku sakonnin da muka samu daga wadanda suka bibiyi Tafsirin Alkur’ani mai girma da muka gabatar a watan Ramadan in sha Allah. Da fatan Allah ya amfanar da mu baki daya, ya buda zukatanmu mu fahimci asalin sakon addinin nan na Musulunci da Manzon Allah (SAW) ya kawo mana a matsayin tsira da rahama da jin kai ga dukkan halitta, Allahumma amin.
–Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke
Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh, ya Shehunmu da sauran daukacin Bayin Allah, muna mika sakon gaisuwa da kuma ziyara ta ‘yan’uwantaka ta Musulunci a dukkanin matakai da Annabi (SAW) ya zo mana da shi na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Bayan haka, muna godiya da irin bayanin da aka yi mana a karatunka na Tafsiri na rana ta 11 a game da muhimmancin karfafa zamantakewa ta wayewar Musulunci a tsakanin Musulmi a duk inda suke. Tabbas, lokaci ya yi da masu wa’azin Musulunci ya kamata su daina kafa hujjar yaki da ayoyin Surar Bara’a a wuraren da ba su dace ba, domin akwai wasu ayoyi da suke da wasu hukunce-hukuncen tare da kawo maslahar zamantakewar al’umma.
Gaskiya ne cewa bai kamata a rika amfani da hukunce-hukuncen Surar Bara’a ba har sai abu ya baci an rasa yadda za a yi a kawo karshen yaki. Inda hakan ne zai sa a yi amfani da salon yaki na ruguza komai bisa dabarun yaki na tsoffin janarorin soja. Idan aka koma wa bin tsarin da musulunci ya kawo, za a daina kashe-kashen musulmi barkatai a wuraren da aka kunna musu wutar yaki wanda wannan ya kasance babban abin da yake ci mana tuwo a kwarya yau a duk fadin duniya
Surarar Bara’a, tana kunshe da wasu umarni na Ukuba kebabbu ga masu gallaza wa Mu’uminai saboda gudun ko-ta-kwana. Abin nufi daga haka shi ne, in ya zama dole ga Musulmai sai sun yi yaki don tsira daga azzalumai, to Suratul Bara’a tana nan tana jiran masu gallaza wa musulmin. Amma in ba haka ba, ayoyin Rahma suna gabanta. Jihadi ba yaki kawai yake nufi ba, yana nufin kokari a kowanne irin al’amari na rayuwar dan Adam amma kalmar Kitali ce ke nufin amfani da takobi wurin yaki (zubar da jini).
Allah ya fada wa Annabi (SAW) cewa, ya Rasulallahi, “Da Ubangijinka ya so, da kowa ya zama Mu’umini”. Kuma a wani wuri, Allah ya kara da cewa, “shin ya Rasulallahi, za ka tilasta wa al’umma ne har sai kowa ya zama Mu’umini”. Don haka babu tilas a Musulunci. Ya kamata mu musulmi musulmi mu karfafa zamantakewa ta wayewa a duk inda muke musamman a birane kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar lokacin da ya yi Hijira zuwa Madina.
Mu nuna kyawawan dabi’u da kyakkyawar mu’amala ta zaman tare a tsakanin al’umma kamar yadda tsarin zama na birni da Annabi (SAW) ya kafa a Madina ya koyar da mu. Annabi (SAW) ya fada mana cewa, “Musulmi nagari shi ne wanda Musulmai suka kubuta daga (sharrin) harshensa (bakinsa) da hannunsa”. Wannan yana kira ne gare mu a kan nuna hali nagari da kyawawan dabi’u na zamantakewa da barin cutar da al’ummar Annabi (SAW).
Kuma ya kamata mu cire bambancin addini da kabilanci wurin zamantakewa da sauran wadanda ba musulmi ba da muke nuna musu kyama, domin wannan shi ne wayewa kamar yadda Annabi (SAW) ya kafa a Madina, inda ya zauna da yahudawa da munafikai har sai da yahudawa suka ci amanar kasa sannan Annabi (SAW) ya kore su daga baya. Duk ka’idojin hakan suna nan a cikin Wasikatu Madina inda Annabi (SAW) ya shirya kyawawn dabi’u da harkokin ci gaban rayuwa.
Allah Ta’ala ya saukar da Littafin Injila don saukaka hukunce-hukunce masu tsauri da ke cikin Littafin Attaura. Duk wannan sauki da Rahma da ke cikin Injila, amma Alkur’ani ya zo da mafi saukinta. Saboda Annabi Muhammad (SAW), ya zo ne da Rahma ga duk halitta, don haka, Addininsa shi ne mafi Rahmar Addinatai amma ba na kisa da yake-yake da nuna muguwar kiyayya ga halittar Allah ba.
Allah yaba mu ikon gyarawa da komawa kan turba ta asali ta Annabi Muhammadu (SAW) ta rahamaniyyarsa da jin kai. Sakona kenan, ya Shehi. Mun gode
Sako daga Ahmadul Badawi Umar
-Mu yaki zuciyarmu ya fi mu dauki makami muna kisan al’umma
Salamullahi alaikum. Akramakallah muna muku ban gajiya da karatun da aka gabatar na Azumin Ramadan, Allah ya sada mu da cikakkiyar ladan amin. Na saurari karatun da ka yi da kuma jan hankalin al’ummarmu a kan mu dawo kan fahimtar addini ta asali tare da daina cakuda fahimtar ma’anar “Jihadu” da “Kitalu” don tunzura musulmi su zubar da jini, musamman ma ganin cewa Annabi (SAW) bai taba daura yaki ba sai don kare kai.
Haka nan, Jihadi na gyaran zuciya shi ne babban Jihadi wanda ya fi wuya fiye da na makami da aka sauya ma’anarsa daga kowane kokari zuwa ma’anar yaki kawai. Shi ya sa Bayin Allah Sufaye da suka fahimci wannan ma’anar daga Manzon Allah (SAW), sai suka dukufa ga gyaran zuciya amma daga bisani wasu suka fito a cikin addini suna cewa duk abubuwan da suke yi na gyaran zuciyar babu kyau, kuma hakan ya tare wasu bayin Allah daga samun gyaruwar zuciya.
Muna kira ga ‘yan’uwa Musulmi a kan mu dawo kan ma’anar jihadi ta asali, kamar yadda muka sani, Annabi (SAW) bai takura kowa a Madina zuwa yakin Badar ba sabida daukar fansa ne a kan kwace wa Muhajirai kayansu, kuma tsarin “constitution” din da ya kafa a Madina domin iya kare kasa ne da ya zama hakki a kan ko wane dan kasa da kuma nuna wayewa, shi ya sa da batun yakin Badar ya taso sai da ya sake kafa kwamitin soja domin ya ba shi shawara me ya kamata a yi.
Kuma idan an duba ma ko a mahangar duniya a wannan zamanin, babu shakka yaki ana yi ne don kare kai bayan maslaha ta ci tura har zuwa lokacin gwabzawa amma ba farad daya kawai ake fara yaki ba.
Kitalu (yaki na zubar da jini) da jihadu (kokari) suna da bambanci inda kitalu ke nufin “Gazwu”, watau kai hari na barna haka kawai ba tare da wani laifi ba, kuma Annabi (SAW) bai taba “Gazwu” ba sai dai “Harbu” ko “Difa’u” wadanda ke nufin kare kai.
Ko da a ka’idar yaki ta wayewa ma, idan an yi galaba a kan abokan gaba sai a dakatar da kisa a kama fursunonin yaki domin biyan fansa ko kuma a bar su saboda Allah. Amma ba a hau mutane da kisa ba-ji-ba-gani ba, kwata-kwata wannan tsari ne na jahilai marasa Imani.
Ina kira ga musamman malamai su ji tsoron Allah wajen canja shari’ar Annabi don muradin kare wani bangare na siyasa ko shugabanci, sannan mu sani cewa sakamakon falalar Allah, yanzu duk abin da aka binne ko aka yi kokarin sauya masa ma’ana sai Kur’ani ya tone.
Haka nan, mun fa’idantu kwarai da kiran da ka yi a kan kara fadada tunani a cikin Alukr’ani mai girma saboda ilimomi da Allah ya zuba mana a ciki musamman ma da kake ba da misali da ayar cikin Suratu Ali Imran ta “zuyina linnasi hubbus shahawati…”. Lallai ya kamata malamai su kara tinani kan ma’anarta, saboda Allah ya yi magana ne a kan “nisa’u” gaba daya ba maza kadai ba kuma Allah da ya girmama dan Adam ba zai hada shi da zangarniyar gero da sauran shahawa ba, sabida da haka a sake duba fassarar da ake wa kalmar “banina” ta ayar, domin a asali Kalmar tana nufin gine-gine ne amma ba ‘ya’ya ba.
Kuma muna godiya da kiran da ka yi a kan bukatar kara nuna tausayi ga duk halitta, domin an ruwaito daga Annabi (SAW) cewa, wata mata ta shiga wuta sabida daure mage ba tare da ba ta abinci ba, to ina kuma ga wadanda ke wa dan adam haka?
Jazakumullahu khairan, Akramakallah.
Sako daga Malam Sabi’u Saifullahi
-Babban makasudin Sufunci shi ne gyaran zuciya
Assalamu alaikum ya Sheikh. Muna mika sakon gaisuwa tare da fatan kuna nan cikin koshin lafiya. Allah ya saka muku da alkhairi da irin wayar mana da kai da kuka yi a karatun Tafsirin da kuka gabatar na Azumin Ramadan na bana. Ni tsokacin da nake so na yi shi ne a kan batun asalin ma’anar sufanci da ka yi bayani a kai, watau kore wa Allah tabaraka wa ta’ala kishiya (Tazkiyya) da kuma koyi da halayen fiyayyen halitta Annabi (SAW).
Hakika, Sufanci yana koyar da dabi’u masu kyau da zama da kowa lafiya, inda karatun sufanci ya fi karkata ga koyar da yaki da zuciya da zubar da ganin kai (Jihadul Kabir), ta yadda za ka bi wani Bawan Allah wanda zai shiryar da kai zuwa ga Allah kuma ya koya maka alaka mai kyau don zama da Bayin Allah. Shehu Hasanul Shazali ya lissafa abubuwa biyar (5) da karatun Sufanci ya rataya a kansu, da suka hada da Muradu, Muridi, Sharadi, Hanya, da Zikirai kafin zuwan Tarbiyyar Failar Shehu Ibrahim Inyass (RTA).
Kuma ga duk wanda zai yi nazari, Sufanci yana nan cikin wannan ayar da Ubangiji ke cewa, “Wa ibadur Rahmanu…” a cikin suratul Furkan. Mu Bayin Allah ne a ‘Ibadu’, ma’ana masu ‘yanci da muke iya yin kuskure ko saba masa kuma mu nemi gafararsa (Arrahmanu), amma da Allah ya ga dama, sai ya mayar da mu, ‘Abidu’ kamar Mala’iku wadanda ba su da ‘yancin yin kuskure ko sabon Ubangiji. Sabon Allah ya rabu kashi biyu: Zanbu da Sayyi’a. Zanbu shi ne sabon bawa tsakaninsa da Ubangijinsa, inda yake iya neman gafararsa (Arrahmanu), amma Sayyi’a na nufin munanawa ko tauye hakkin Bayin Allah. Nan kuma, dole Shari’a sai ta yi hukunci kan mai zalunci.
Ya Sheikh, muna godiya da wasu abubuwa na sha’awa fiye da 10 da suke cikin halittar bil’adama da ba a iya ganinsu a zahiri sai dai ayyukansu da ake kira da “Gariza” wadanda ka lissfto mana a zaman karatun Tafsirin na 13. Tabbas, wadannan abubuwan dan ‘Adam yana gudanar da su a rayuwarsa ta yau da kullum saboda bukatarsa gare su.
Allah ya kara ilimi da fahimta, ya ba mu iko da karfafa mu a kan aiki da wadannan ilimomi da hikimomi da ka kawo mana. Was salamu alaikum wa rahmtullah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp