Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya yi fatali da batun dawo da tallafin man fetur, wanda a cewarsa zai kara ta’azzara talauci.
Dawo da tallafin man fetur na daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar #EndBadGovernance.
- ’Yansanda Sun Cafke Karin Mutane 82 Kan Zanga-zangar Yunwa A Jigawa
- ‘Yansanda Sun Ja Hankalin Jama’a Kan Su Guji Rikiɗewar Zanga-zanga Zuwa Rikici A Ribas
Sai dai a jawabin da ya yi a fadin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da batun mayar da tallafin, inda ya ce, cire tallafin akwai radadi amma ya zama dole.
Da yake magana a wani shirin na gidan Talabijin na ‘Sunrise Daily’, a ranar Laraba, Issa-Onilu ya shawarci ‘yan Nijeriya da su tsara yadda ya kamata su yi rayuwa a cikin tabarbarewar tattalin arziki na cire tallafin man fetur.
“Duk wanda ke neman a dawo da tallafin da aka cire, son kai ne kawai ba kishin tattalin arzikin kasa, idan aka dawo da shi, ba zai magance matsalar talauci ba, fa ce, talauci ne zai tsananta.”