Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kammala daukar mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Matthijs de Ligt kuma dan wasan dan asalin kasar Holland ya amince da kunshin kwantiragin da zai kare ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2027.
Dan wasan wanda an yi ta alakanta shi da cewar zai koma Manchester United ko Barcelona ko kuma Paris-St Germain da buga wasa ya je kasar Jamus a karamin jirgin sama kuma ya bayyana cewa yana cike da murna kasancewa sa a kungiyar ta Munich.
Dan wasan ya fara buga wasa a shekarar 2016 ya kuma lashe Eredivisie da Dutch Cup ya kuma buga wasan karshe a Europa League a 2017, sannan De Ligt ya ci kwallo takwas a wasanni 77 a Ajax, kungiyar da ya koma buga wasa yana da shekara tara, kuma ya zama matashin kyaftin din kungiyar a watan Maris din shekara ta 2018.
Shi ne ya ci kwallon da Ajad ta doke Juventus ta kai wasan dab da karshe a Champions League, inda ta yi rashin nasara a hannun Tottenham sannan yana wakiltar kasar Holland a wasanni da dama.