Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta bayyana goyon bayanta ga sabon tsarin babban bankin Nijeriya na sauya fasalin Naira da kuma takaita mu’amala da tsabar kudi, inda tace bai kamata ‘yan Nijeriya su bar tsabar kudi a hannun masu sana’ar kwayoyi da azzaluman ‘yan canji da ‘yan kasuwa ba.
Kungiyar daliban ta kuma bukaci babban bankin kasa CBN da ya samar da isassun matakai masu tsauri da za su ceto darajar Naira.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a baya-bayan nan an yi ta samun wasu gungun magoya baya da kuma adawa da sabbin manufofin Bankin CBN.
Sai dai yayin da yake mayar da martani game da ci gaban a ranar Talata ta hanyar wata sanarwa bayan taron gaggawa na shugabannin kungiyar da aka gudanar a karshen mako, inda aka yi tsokaci kan batutuwan da suka dame daliban Nijeriya da kuma yadda lamarin zai shafi rayuwar daliban. kungiyar daliban ta bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi canjin, sannan kuma ta nemi bankuna da su sa ke inganta aikace-aikacensu ta yanar gizo don karfafa kwarin gwiwar masu amfani da su.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar daliban ta kasa NANS, Kwamared Felix Attah Nnalue, ta ce Nijeriya a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki da yawan al’umma a Afirka amma ta samu hauhawar farashin canji da ba za a taba mantawa da shi ba a cikin shekaru bakwai da suka gabata, ya kamata a shawo kan lamarin.