Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku da Okowa, Sanata Dino Melaye ya yanke jiki ya fadi a filin wasan kwallon kafa na Stephen Keshi.
Dino ya fadi ne a lokacin da yake zolayar dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC sanata Bola Ahmed Tinubu.
Lamarin wanda ya afku a jiya talata, Dino ya fadi a kas ne a yayin gangamin yakin zaben ‘yan takarar a garin Asaba da ke a jihar Delta.
Faduwar ta Dino wacce ke a cikin wani faifan bidiyo an gan shi yana zolayar Tinubu, inda Dino ke nuna Tinubu bai da koshin lafiya.
‘Yan jamiyyar PDP dai na ci gaba da magana akan lafiya da takardun makarantar Tinubu.