Dogariyar ‘yar sandan matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Sufeto Hassana Sule, ta kwanta dama.
Ta yi hidima ga gwamna kimanin shekaru bakwai a matsayin mai bada kariya.
- Bayern Munich Ta Dakatar Da Sadio Mane
- Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Bunkasa Da Kaso 4.8% A Rubu’in Farko Na Bana Duk Da Raguwar Bukatun Waje
Marigayiya Sufeto Hassana Sule, ta rasu ne a daren Talata 11 ga watan Afrilu, 2023 bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya a jiharta ta Kogi.
Kawarta Balkisu Sule ce ta sanar da rasuwarta.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
A cikin sakon ta’aziyyarta, matar gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zanab Shinkafi Bagudu, ta bayyana matukar kaduwarta bisa rasuwar Jami’ar.
Ta yi ta’aziyya ga ‘yan uwanta da abokan arziki kan rashin da suka yi.
Ta kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayiyar da rahama, ya sanya ta a Aljanna Firdausi, ya kuma bai wa ‘yan uwa hakurin jure rashinta.
A halin da ake ciki, an aike da wata babbar tawaga karkashin jagorancin jami’in hulda da jama’a mai kula da masaukin gwamnatin Jihar Kebbi da ke Abuja, Alhaji Ibrahim Garba domin ta’aziyya ga iyalanta.