Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya tunatar da shugaban rikon kwarya na Jihar Ribas, Bice Adimiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, kan iya hurumin da yake da shi na shugabancin wannan rikon kwarya, karkashin dokar ta-baci a halin yanzu.
Shugaban majalisar, ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da wani kwamitin wucin-gadi mai dauke da wakilai 21, wanda aka dora wa alhakin sa ido kan harkokin mulki a jihar, inda aka dakatar da tsarin demokuradiyya, sakamakon ayyana dokar ta-baci da shugaban kasa ya yi.
- Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
- Alkaluman Tattalin Arzikin Sin Sun Shaida Dorewar Ingancin Tattalin Arzikinta
Yayin da yake bayyana makasudin kafa kwamitin, Kakakin Majalisar Abbas ya bayyana cewa, aikinsa zai kasance a matsayin, “Sa ido kan yadda ake aiwatar da umarni da kuma tsare-tsaren gwamnatin tarayya a jihar ta Ribas, tabbatar da cewa; gwamnatin rikon kwarya tana bin doka da kare muradun jama’a tare kuma da samar da damar sake kafa cikakken mulkin demokuradiyya.
Ya jaddada cewa, dole ne ayyukan shugaban rikon kwaryar su yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar, tare kuma da tabbatar da aiwatar da gaskiya da rikon amana.
“Ana bukatar shugaban rikon kwaryar, ya gudanar da mulkinsa cikin girmamawa da kuma gaskiya da rikon amana, sannan ya kasance yana bayar da rahoto kai tsaye ga majalisar dokoki ta kasa, kan dukkanin al’amuran da suka shafi zaman lafiya da kuma ci gaban da aka samu a gwamnatin jihar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada”, in ji shi.
Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da rusa majalisar dokokin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp