Kwanan baya, an kira taron koli karo na 3 na kawancen kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CELAC da EU a Brussels, wani jami’in kasar Argentina ya shedawa manema labarai cewa, wannan shi ne karon farko da EU ta ambaci batun tsibiran Malvinas a cikin dogon lokaci.
Wato an ambaci batun ikon mulkin tsibirai a cikin sanarwar taron, hakan ya sa bangarorin biyu za su warware wannan matsala ta hanyar shawarwari cikin lumana bisa tushen mutunta dokar kasa da kasa.
Wannan shi ne karon farko da wadannan manyan kungiyoyi biyu na shiyya suke ambaton batun ikon mulkin tsibirai a cikin sanarwar tasu. EU na nuna cewa, ta fahimci matsayin da CELAC ta dauka kan batun, kuma ta nanata alkwarin da ta yi kan ka’idoji da abubuwan da aka tanada a cikin tsarin mulkin MDD.
Ban da wannan kuma, sanarwar ta Turanci ta amfani da sunan da Argentina ta sanyawa tsibirai wato “Malvinas Islands”. Argentina ta bayyana farin ciki kan batun, a cewarta, nasara ce da ta samu a fannin diplomasiyya.
Amma, a wani bangare, Birtaniya ta fusata matuka, inda ta kira zabin kalmomi a cikin sanarwar da cewa abin takaici ne. Kafofin yada labaran Amurka sun ce, Birtaniya ta yi kokarinta wajen hana kungiyar EU ambaton tsibiran Malvinas a cikin sanarwar da ta yi, amma abin ya ci tura. (Amina Xu)