Darakta Janar na Rundunar tsaro ta farin kaya, DSS, Oluwatosin Ajayi, ya bayyana bukatar bai wa al’umma damar mallakar wasu makamai domin bin wasu matakan kare kansu daga ‘yan bindiga.
Ajayi ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron shekara-shekara na kungiyar tsofaffin daliban Cibiyar Nazarin Tsaro ta kasa (AANISS), mai taken, “Tafiya da masu ruwa da tsaki don dakile matsalar rashin tsaro a Nijeriya: a aikace,” a Abuja.
- Kalaman Trump Marasa Kan-gado Game Da Gaza Za Su Kara Tsananta Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta tsakiya
- Ku Gafarce Ni, Na Yi Nadamar Tallata Tinubu Da Na Yi – Ɗanbilki Kwamanda
Da yake bayar da misali da mutanen ‘Siawas’ da ‘Azare’ a jihar Bauchi, shugaban hukumar DSS ya ce, mutanen yankin sun iya kashewa tare da korar dukkan maharan saboda sun san yankinsu.
“Ba wai kawai sun fatattake su ba ne, sun kwace makamansu, kuma tun a wancan lokacin, har yanzu, zai yi wuya ka ji wani labarin mahara a Tafawa Balewa, don haka, shawo kan kalubalen tsaro, dole sai an saka duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin lamarin.
“Tsammanin sojojin Nijeriya, ‘yansanda, ko DSS, za su kare kowane dan Nijeriya ko kowace gwamnati, Hakan ba zai yi wu ba,” in ji shi.
Ajayi ya kara da cewa, dole ne kasar ta samar da matakan tsaro domin rage nauyi a kan tushen tsare-tsaren tsaron kasa.