Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai na yau Litinin cewa, tsirarrun kasashe ne kawai a duniya ciki har da Palau, ke ci gaba da yin abin da suke kira “dangantakar diflomasiyya” da yankin Taiwan, lamarin da ba kawai ya sabawa muradunsu da muradun jama’arsu da kuma kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2758 ba, har ma ya sabawa ikon mulkin kasar Sin, kuma ya kamata su gyara.
Mao ta yi nuni da cewa, kasashe 183 a fadin duniya sun riga sun kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin bisa ka’idar Sin daya tak a duniya. Kana ba za a iya dakatar da wannan gagarumin amincewa da ka’idar ba.
Mao ta kara da cewa, kasar Sin tana kira ga wadannan kasashe da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a karkashin dokokin kasa da kasa, da tabbatar da gaskiyar tarihi, da yanke shawarwari masu dacewa da muradunsu na asali da na dogon lokaci bisa gaskiya tun da wuri. (Yahaya)