A yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Da take tsokaci dangane da furucin da ministan harkokin wajen Jamus ya yi a baya-bayan nan kan halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, Mao Ning ta bayyana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata ka’ida mai tushe da asali a cikin dangantakar kasa da kasa, kuma babbar matsaya ce da kasashen duniya suka cimma. Domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, dole ne a tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak ba tare da wata shakka ba, tare da nuna adawa da ayyukan yunkurin neman “’yancin kan Taiwan”. Ban da haka, ta kuma karyata kalaman da jami’in kula da harkokin waje na yankin Taiwan ya yi, inda ta yi nuni da cewa, furucin nasa ya sake nuna yadda gwamnatin Lai Ching-te ke da cikakken goyon bayan neman “’yancin kan Taiwan”.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Tallafin Kuɗi Ga Talakawa 2.2m – Minista
- Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Zartar Da Dokokin Bunkasa Kasa Tun Daga Shekarar 2021
Dangane da batun yadda Australiya ta ba da kariya ga masu adawa da Sin a yankin Hong Kong kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su mutunta ikon mulkin kasa ta Sin da dokar mulkin Hong Kong, da kuma dakatar da duk wani nau’i na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin.
A game da ganawar da Vladimir Vladimirovich Putin da Donald Trump suka yi a baya-bayan nan, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokari da ake yi wajen warware rikici cikin lumana, kana tana maraba da ci gaba da hulda tsakanin kasashen Rasha da Amurka.
Har ila yau, Mao Ning ta yi bayani kan ziyarar da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi zai yi a Indiya tare da gudanar da taron wakilan musamman kan batun iyakar Sin da Indiya karo na 24.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp